Birnin Bor ya fada hannun sojan gwamnati | Labarai | DW | 18.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birnin Bor ya fada hannun sojan gwamnati

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun tabbatar da ficewa daga tungar su, bayan da sojan gwamnatin Salva Kiir da hadin gwiwar sojojin kasar Yugunda suka yi musu luguden wuta.

Dakarun dake biyayya ga shugaban kasar Sudan ta Kudu, da ke samun agaji sojojin kasar Yuganda, sun tabbatar da kwato birnin Bor daga hannun yan tawayan kasar a Asabar din nan.

Birnin na Bor dai na daya daga cikin cibiyar rikicin kasar ta Sudan ta Kudu, inda ake ta gwabza fada tun watan Disamba da ya gabata.

Dakarun na SPLA masu biyayya ga gwamnatin kasar, sun shiga cikin birnin na Bor da ke a nisan kilo mita 200 a arewacin Juba babban birnin kasar. A cewar Philip Aguer kakakin sojan kasar ta Sudan ta Kudu, dakarun su na SPLA sun fatattaki 'yan tawayen da yawan su ya kai a kalla dubu goma sha biyar, masu biyayya ga Tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, da ke a matsayin madugun 'yan tawayan. Wanda hakan ya karya lagon yan tawayen da ke da aniyar aukawa ya zuwa birnin na Juba. Tuni dai Mr Ateny Wek Anteny, kakakin fadar shugaban kasar ta Sudan ta Kudu ya jinjinawa sojojin, inda ya ce sun yi gagarumin aiki na yabo tare kuma da kiran dakarun sojan kasar da su kiyaye bin doka da oda.

Mawallafi: Salisou Boukari

Edita: Usman Shehu Usman