1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birnin Bambari ya fada hannun 'yan tawaye

Mouhamadou Awal Balarabe
December 22, 2020

Hukumomin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun bayyana cewar 'yan tawaye sun kwace birnin Bambari da ke da nisan kilomita 380 da Bangui babban birnin kasar bayan arangama da dakarun gwamnati.

https://p.dw.com/p/3n7De
Karte Zentralafrikanische Republik Bouar, Bangui, Bambari Englisch
Hoto: DW

 Jami'an gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da na Majalisar Dinkin Duniya da kuma magajin garin Bambari suka ce an yi musayar wuta na sa'o'i biyu tsakanin 'yan tawayen da sojojin kiyaye zaman lafiya na Minusca kafin birnin da ke zama na hudu a girma a kasar ya fada hannu 'yan bindiga. Dama tun da sayin safiyar ranar talata ne fada ya sake barkewa a garin na Bambari tsakanin masu dauke da makamai ta UPC da sojojin gwamnati.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta sanar da cewa ta tura da kari sojoji 300 zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin taimaka wa gwamnatin kasar tinkarar farmaki da kungiyoyin ‘yan tawaye suka kai wanda ta danganta da yunkurin juyin mulki. Ita Rasha ta nuna damuwa matuka game da rikicin siyasa da na tawaye da ke faruwa a 'yan kwanakin da suka gabata, gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.