Binciken mutuwar Sankara a kasar Faransa | Labarai | DW | 16.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken mutuwar Sankara a kasar Faransa

Mariam Sankara ta bayyana wannan bukata tata ce lokacin wata ziyara da ta kai a majalisar dokokin Kasar Faransa a ranar Talata.

Mai dakin tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara ta bukaci 'yan majalisar dokokin Kasar Faransa da su gudanar da bincike na kansu domin tantance rawar da kasar ta Faransa ta taka cikin kisan mai gidan nata wanda sojojin kasar ta Burkina Faso suka hallaka a lokacin wani juyin mulki da suka yi masa a shekara ta 1987.

Mariam Sankara wacce ta kai wata ziyara a ranar Talata a majalissar dokokin Faransa tare da rakiyar lauyanta ta ce tana bukatar wannan bincike ne domin kuwa kawo yanzu daga cikin wadanda ake zargi da hannunsu a cikin kisan mai gidan nata so tari a kan ambato sunan kasar Faransa.

Wannan bincike na 'yan majalissar dokokin ta Faransa za ya iya bada damar bincikar cibiyoyin ajiyar takardun tarihin kasar ta Faransa domin samun karin haske a kan mutane ko kuma kasashen da suka yi ruwa da tsaki wajen kashe mai gidan nata. A lokacin aukuwar lamarin dai Faransa na a karkashin jagorancin shugaban kasa Francois Mitterand da Firaminista Jacques Chirac.