Binciken kisan fararen hula bara a Burkina | Labarai | DW | 15.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken kisan fararen hula bara a Burkina

Kungiyar Amnesty International ta bukaci da a gudanar da binciken gano sojojin da suka murkushe masu boren da ya hambarar da gwamnatin Compaore.

Kungiyar kare 'yancin bani Adama ta duniya Amnesty International, ta bukaci yin cikakken bincike kan murkushewar da sojoji suka yiwa masu zanga-zangar a Burkina Faso wadda ta kaiga hambare gwamnatin shugaban kasar Blaise Campaore a bara.

A cewar kamfanin dillacin labaran Faransa AFP, wani binciken da kungiyar ta gudanar, ya gano cewa sojin na Burkina, sun kashe akalla masu zanga-zangar su 24 ciki har da wasu 'yan fursuna biyar da masu gadin su suka kashe, tare da jikkata daruruwa.

Wani binciken har ila yau da Faraiministan Burkina Fason Isaac Zida ya kafa ya tabbatar da hakan tare da bayyana yawan wadanda suka jikkata i zuwa mutane 625.

A ranakun 30 ga watan Oktoba zuwa 2 ga Nuwambar bara ne dai, 'yan kasar ta Burkina suka yi boren da ya kifar da gwamnatin tsohon shugaba Blaise Campaore.