1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

030209 Dialog Islam-Lehrer

Mohammad AwalFebruary 19, 2009

Wani bincike da aka gudanar a ƙasar Austriya ya janyo kace-nace domin sakamakonsa ya nunar da cewa kimanin kashi 22 cikin 100 na waɗanda aka yiwa tambayoyi sun nuna adawa da tsarin mulki na demoƙuraɗiyya.

https://p.dw.com/p/Gx9J
Majami´ar Stephan a Vienna babban birnin AustriyaHoto: picture-alliance/ dpa

Sakamakon wani binciken jin ra´ayin jama´a da wani masanin kimiyar addinin musulunci a ƙasar Austriya, Mouhanad Khorchide ya gudanar yayin aikinsa na neman digirgir, ya ta da hankalin jama´a ƙwarai da gaske. A jerin tambayoyin da ya aikewa malamai har da yadda suke ɗaukar tsarin mulkin demoƙuraɗiyya da batun ´yancin ɗan Adam. Fiye da kashin 50 cikin 100 na waɗanda aka aikewa tambayoyi sun ba da amsa. To sai dai an yi mamakin sakamakon wannan binciken.

Wai shin mene ne ra´ayin malaman addinin musulunci a Austriya? Mene ne matsayinsu game da demoƙuraɗiyya da batun kare haƙin ɗan adam? Waɗannan dai sune tambayoyin da masanin addinin na musulunci Mouhanad Korchide dake zaune a birnin Vienna ya nemi ƙarin bayanin kansu a cikin aikin sa na neman digirgir. Shi kanshi yayi mamakin sakamakon da ya samu inda ya nuna damuwa game da halin da ake ciki.

“Abin da muka gano shi ne malaman addinin na matsayin wakilai na addinan su. Suna ɗaukar aikinsu a matsayin masu koyar da yaran makaranta dukkan abubuwan da addinan suka ƙunsa.”

A halin da ake ciki akwai malaman addinin musulunci fiye da 380 a ƙasar ta Austriya, kuma kimanin 200 daga cikinsu suka shiga cikin binciken jin ra´ayoyin da aka gudanar. Kashi 22 cikin 100 daga cikinsu sun nuna adawa da tsarin mulkin demoƙuraɗiyya saboda rashin dacewarsa da addinin musulunci, sannan kashi 27 cikin 100 suka yi fatali da batun kare haƙin ɗan Adam yayin da kuma kashi 18 cikin 100 na musulmin da aka yiwa tambayoyin suka goyi da bayan aiwatar da hukuncin kisa kan waɗanda suka yi ridda.

A taƙaice mutumin da ya gudanar da wannan bincike ya gano cewar kashi ɗaya cikin biyar na malaman addinin musulunci a Austriya na da zazzafan ra´ayi. Sakamakon wannan binciken dai ya ta da hankalin gamaiyar musulmin ƙasar ta Austriya wadda ke wakiltar dukkan al´umar musulmai kimanin dubu 400 a wannan ƙasa, wadda kuma har wa yau ita ke sa ido akan darussan addinin a makarantu.

Shugaban gamaiyar musulman Anas Schakfeh ya nuna shakkunsa game da sakamakon binciken inda ya bayyana shi da cewa bai da tushe bare makama. Ya ce a matsayinsu na masu ɗaukar malaman addininn musulunci aiki ko kaɗan gamaiyarsu ba za ta taɓa jurewa hallayar nuna adawa da tsarin mulkin demoƙuraɗiyya ba.

“Idan muka gano cewa wani malami ko wata malama a makarantunmu na da irin wannan ra´ayi to zamu yi gaggawan ɗaukar matakin da ya dace akansu.”

Anas Schakfeh ya ci-gaba da cewa malamai na da ´yancin nuna adawa da tsarin na demoƙuraɗiyya a cikin zamansu ko rayuwarsu a gida amma ba za a amince sun yaɗa wannan matsayin na su a tsakanin yaran makaranta ba. Shi ma Adnan Arslan Farfesan addinin musulunci a jami´ar birnin Vienna ya kwatanta wannan matsayin tamkar wani baƙon abu a duniya inda ya ce.

“zai yi wuya in tabbatar da wannan abu a aikace, domin addini ba wani saƙo ne na fasaha ba, shi fa addini wani abu ne da ya shafi imaninka a zucci.”

Hukuma ce ke biyan albashin malaman addinin musulunci a ƙasar ta Austriya. Kuma tun a shekara ta 1982 aka fara koyar da darussan addinin a cikin makarantun gwamnati. A wancan lokaci da aka ɓullo da wannan darasin an fuskanci matsalar ƙarancin malamai domin malaman addinin muslunci ƙalilan ne ke da shaidar samun ilimi da ya dace da matsayin ƙasashen Turai. Ita ma ma´aikatar da ke kula da manhajar makarantun ba ta da ta cewa kan abubuwan da ake koyarwa. Da hakan dai ya saɓawa dokokin tsarin mulkin ƙasar wanda ya raba batun addini da dokokin ƙasa. A halin da ake ciki ministar ilimi Claudia Schmied ta nuna bukatar da a tura mata da rahoton gamaiyar ta musulman.

“A Austriya an tabbatar da ´yancin tafiyar da addini ba da wata tsangwama ba. To sai dai wannan ´yanci na ƙarewa a daidai wurin da dokokin ƙasar suka fara.”

Shi ma magajin garin birnin Vienna kuma shugaban jam´iyar SPÖ Michael Häupl ya tofa albarkacin bakinsa kamar haka.

“Idan na samu sakamakon binciken game da malaman a Austriya to ba zan yi sako-sako wajen ɗaukar matakan da suka dace ba. Ko da yake ba abu ne mai sauƙi ba, amma a ƙarshe za mu fara wata muhawwara game da yiwa tsarin koyarwa kwaskwarima. Ko shakka babu za mu goyi bayan yin gyaran fuska ga tsarin horas da malaman addini wanda hukuma ke ɗaukar nauyin gudanarwa.”

Wannan tsarin koyarwar dai na ƙarƙashin wata yarjejeniya ce da aka ƙulla tsakanin gwamnatin Austriya da fadar Vatikan, wadda ta daidata raba batutuwan da suka shafi majami´ar Katholika da kuma ƙasar ta Austriya. Abin da magajin garin na birnin Vienna yake nufi shi ne duk wata kwaskwarima da za a yiwa tsarin malaman addinin musulunci za ta yi tasiri akan malaman wasu addinan daban. In ba haka ba sai dai ƙasar ta janye amincewar da ta yiwa addinin na musulunci a matsayin wata gamaiyar addini a Austriya kimanin shekaru 100 da suka wuce. Batun da kawo yanzu dai jam´iyar masu matsanancin ra´ayin ƙyamar baƙi ta FPÖ ce kaɗai ke goyawa baya.