1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da bincike kan hadarin jirgin saman Rasha

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 8, 2015

Masu bincike kan musabbabin hadarin jirgin saman kasar Rasha a Masar, sun bayyana cewa suna da yakinin karar da aka ji cikin na'urar nadar bayanan jirgin ta fashewar bom ce.

https://p.dw.com/p/1H1zr
Jirgin saman Rasha da ya tarwatse a Masar.
Jirgin saman Rasha da ya tarwatse a Masar.Hoto: picture-alliance/dpa/Str

Daya daga cikin masu gudanar da binciken wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters, suna da yakini cewa kaso 90 cikin 100 na karar da aka ji cikin na'urar nadar bayanan jirgin ta afku ne sanadiyyar fashewar bom. Jirgin samfurin A321 na kasar Rasha ya yi hadari a mintuna 23 da tashinsa daga wajen yawon bude idanu na Sharm al-Sheikh na kasar Masar a kan hanyarsa ta zuwa birnin St. Petersburg na kasar Rasha dauke da mutane 224 wadanda baki dayansu suka rasa rayukansu a hadarin.