Bincike ya nuna cewar an kakaɓo jirgin MH 17 | Labarai | DW | 09.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bincike ya nuna cewar an kakaɓo jirgin MH 17

Wani sakamakon bincike na farko na nuna cewar jirgin saman nan, na Malaysia wanda ya tarwatse a tsakiyar watan Yulin da ya gabata a gabashin Ukraine an harbo shi ne.

Jirgin wanda ya tashi daga Amsterdam ɗauke da fasinja 298 yawancisu 'yan ƙasar Hollande zuwa Kuala Lumpur, babu wanda ya tsira da ransa a cikinsu. Da yake mayar da martani wani jagoran 'yan tawayen ya ce ba su da irin wannan makamai na zamani waɗanda ke iya kakaɓo jirgin saman.

An harbo jirgin ne a sa'ilin da yake sama inda wani makamin na nukiliya ko roka ta huda jirgin. Mnistan shari'a na Malaysia ya ce dole ne a yi shari'a.

''Ina yin kira ga ƙasashen duniya da waɗanda wannan hatsari ya shafa, da ka da su yi sako-sako, wajen ganin an bin hanyoyin da suka dace na shari'a domin hukunta masu hannu a cikin lamarin.''

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu