Bincike kan kisan wasu matasa a Najeriya | Siyasa | DW | 07.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bincike kan kisan wasu matasa a Najeriya

Jami'an hukumar tsaro ta Najeriya sun yi bayani bisa zargin kisan da ta saba ka'ida wa wasu matasa takwas a Abuja babban birnin Najeriya

Jami'an hukumar tsaro ta SSS da ke Najeriya sun yi bayanai, a ci gaba da binciken da ake yi kan zargin kashe matasa takwas, a unguwar Apo da ke Abuja, bisa zargin cewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne, bincike da ke ci gaba da daukan hankalin kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

An gudanar da tambayoyi na kwakwaf ga wadanda suka ba da shaida, da ma jami'an na hukumar tsaro ta farar kaya a wajen zaman bin bahasin da aka yi a Abuja. Wannan zama da ya biyo bayan turjiya da jami'an hukumar tsaron ta kasa suka yi tun farko, na bukatar ba da shaida a asirce a kan zargin cewa an kashe matasan guda takwas a unguwar ta Apo da ke Abuja ba bisa doka ba, abin da suke musanta hakan.

Daukacin tawagar jami'an hukumar kula da kare hakkin dan Adam da ke gudanar da binciken, ta dunguma zuwa gidan da aka yi wannan kisan a watan Satumban da ya gabata inda aka yi wa jami'an hukumar tambayoyin don bayyana zahirin gaskiyar abin da ya faru. Daraktan kula da gudanarwar ta hukumar tsaro ta SSS din wanda ya wakilci babban daraktan Ita Ekpeyoung, ya kuma amsa tambayoyin kamar haka.

Ya ce "Shi Sulaiman R Kelly da ake tuhuma mun samu bayanai yana da bindigogi kirar AK 47 har guda hudu kuma a kan wannan bayanai da muka samu ne aka fara harin da muka kai a kan wannan gini."

Ganin yadda wannan bincike ke daukan sabon salon a kokarin bayyana zahirin abin da ya faru, kama daga mutanen da suka samu tsira da rayyukansu a lokacin da aka kai wannan hari da ma wadanda hukumar ke tsare da su bisa zargin cewa suna da masaniya a kan wannan batu, Malam Gambo Idris na cikin wadanda suka tsira daga harin, ya kuma yi wa 'yan kwamitin bayanin zahirin abin da ya sani.

Na tambayi Farfesa Bem Angwe na hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriyar don jin shin ina suke a yanzu a kan wannan bincike?

Ya ce "Ba wai zamu ci gaba da wannan bincike a asirce ba, jami'an hukumar tsaro ta SSS, sun gabatar da bayanai a bainar jama'a tare da shaidar wanda suke tuhuma, kuma ina tabbatar wa 'yan Najeriya cewa hukumarmu za ta tsage gaskiya da adalci."

Zargin kashe mutanen takwas ba bisa doka ba a unguwar ta Apo da ke Abuja na ci gaba da daukan hankalin jama'a musamman bayan da 'yan uwan mutanen suka shiga korafi a gaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya wacce ta sha alwashin bankado gaskiyar da ke tattare da lamarin.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin