Bincike kan hadarin jirgin kasa a Spain | Labarai | DW | 26.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bincike kan hadarin jirgin kasa a Spain

Masu bincike a kasar Spain kokarin lalubo musabbabin hadarin jirgin kasan da ya afku a kasar, in da ake danganata hadarin da gudun wuce sa'a.

Ana tsammanin direban jirgin kasan nan da ya yi hadari a ranar Alhamis a kasar Spain na sheka gudun da ya wuce kima ne, wanda ake kyautata zaton hakannne ya haddasa hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 80 tare da raunata wasu 140.

Wani faifan Vidio a kan hadarin jirgin, ya nuna cewa jirgin ya shiga wani guri da aka kiyasta nisansa da tsahon Kilomita 80 da gudun da a kallah ya ninka wanda ake bukata yayin tuki sau biyu.

A jawabin sa yayin da ya kai ziyara inda hadarin ya afku, Firaministan kasar Mariano Rajoy ya jajantawa Iyalai da 'yan uwan wadan da hadarin ya rutsa da su yana mai cewa...:

" Da sunana, da yawun gwamnatin kasar Spain da kuma dukkan 'yan kasar da suke tayamu jimamai, ina so in mika jajena ga 'yan uwa da abokan arzikin wadanda wannan hadari ya rutsa da su da suke da yawan gaske".

Rajoy ya bayyana kwanaki uku na zaman makoki a kasar, ya yin da masu bincike ke cewa suna gudanar da bincike domin lalubo sanadiyar hadarin don su tabbatar da cewa, ko ya faru ne sakamakon gangacin da matukinsa ya yi ko kuma wata matsala da ake zargin bangaren lura da gudun jirgin na da ita.

Maawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita Umaru Aliyu