1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike kan amfani da guba a Douma

April 8, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya sake kaddamar da bincike kan kasashen da ke da hannu cikin hari da guba a gabashin Siriya.

https://p.dw.com/p/2vgiy
Syrien Kinder werden nach möglichem Giftgaseinsatz in Douma behandelt
Hoto: picture alliance/AP Photo/Syrian Civil Defense White Helmets

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kiran daukar matakai kan amfani da makamai masu guba da dakarun gwamnatin kasar Siriya suka yi kan Douma da 'yan tawaye ke rike da shi. Kungiyar musamman ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya sake kaddamar da bincike kan kasashen da ke da hannu cikin lamarin, musamman Iran da Rasha da ake nuna wa yatsa.

Gwamnatin Siriya dai ta karyata zargin da aka yi wa dakarunta da yin amfani da makaman masu guba a garin na Douma. Ita ma dai kasar Rasha ta yi fatali da zargin a jerin hare-haren da aka kai ta sama kan 'yan tawayen kasar a tungarsu ta birnin na Douman jihar Goutha da ke wajen birnin Damascus.