Bikin tunawa da faduwar katangar Berlin a 1989 | Siyasa | DW | 09.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin tunawa da faduwar katangar Berlin a 1989

Yankunan yammaci da gabashin Jamus na tattauna batun saukake zirga-zirga tsakaninsu ne ba zato ba tsammani jama'a suka taru suka rusa katangar na Berlin da ta haramta musu shige da fice.

Ba zato ba tsammani, katangar Berlin ya fadi, bayan da aka shafe shekaru 28 ya na raba mutanen yammacin Jamus, da 'yan uwansu da ke yankin gabashin kasar. A wancan lokacin dai yankunan biyu sun yi ta tattaunawa dangane da bude iyakokinsu domin samar da damar shige da fice. to sai dai daga baya, yadda aka yi bangon ya fadi, ya kasance tamkar wani abun da ake gani a cikin majigi.

Ranar 29 ga watan Oktoba, ya kasance ranar Lahadi, Walter Momper magajin garin yammacin Berlin ya na yankin gabashin. Ziyarar tasa dai ba ta boye ba ce, amma kuma ba a hukumance ba ne. Wani mutun mai suna Manfred Stolpe shugaban Cocin Jamhuriyar Demokiradiyyar Jamus ne ya gayyaceshi cin abincin rana, kuma ya kasance tare da manyan yankin guda biyu harda Günter Schabowski, suna tattauna wata sabuwar doka ta tafiya wanda kwanaki hudu bayan nan ma wata jarida mai suna Neues Deutschland ta rubuta kuma kowa ya karanta.

Willy Brandt 1989 Schöneberger Rathaus Berlin

Willy Brandt da Walter Momper wuni daya bayan faduwar katangar Berlin

Dokar dai za ta saukake zirga-zirga tsakanin yankunan biyu kuma wannan taron dan tattauna yadda za ta fara aiki ne kafin bukin Kirisimati, inda ake sa ran mutane da yawa za su shiga yankunan biyu. Wannan ci gaban dai ya faranta wa Momper, magajin garin yammacin Jamus din rai sosai, kamar yadda masanin tarihi Hans-Hermannn Hertle ya bayyana a wata hirar da ya yi da tashar DW.

Sai dai daga ranar 3 ga watan Nowamba wannan tattaunawa tasu ta fito a fili, aka dago cewa Momper ya na ganawa da jagororin yankin gabashin,daga nan ne Harry Gilmore, babban jakadan Amirka a yammacin Jamus ya bukaci Momper ya bayyana abin da ya yi cikin sirri.

Ganawar Sirri

Dr. Hans-Hermann Hertle

Masanin tarihi Dr. Hans-Hermann Hertle

Ba kowa ba ne ya san batun cewa magajin garin yammacin Berlin din ya bi bayan Faransa da Birtaniya da Amirkawa ya gana da takwarorinshi na yankin gabashin ba. Manyan mutane biyu ne a wancan lokacin, suka kasa fahimtar wannan dangantaka, a cikinsu akwai Horst Teltschik, babban mai baiwa Helmut Kohl shawara lokacin da ya kasance shugaban gwamnatin Jamus, wanda ya ce bai ma taba sanin cewa an taba yin wannan tattaunawa ba

"Ina jin wannan ne a karon farko. Ba zan iya tuna ko an yanke shawara ko kuma ma an yi tunanin bude iyakokin kafin faduwar bangon Berlin ba"

Momper bai tsaya a nan ba, ranar 6 ga watan Nuwamba ya rubutawa shugaban gwamnatin Jamus na wancan lokacin, Helmut Kohl wasika, domin ba tare da Berlin ba, kudaden dole su fito daga Bonn, ya bukaci da a tura wa gwamnatin DDR kudi saboda wadanda suke so su yi tafiya, wanda ya nuna kuma yana bukatar ya gana da Kohl.

29.10.2014 DW DOKU Schabowskis Zettel 2

Günter Schabowski, mutumin da ya kafa tarihi

Bukatar ganawa da Helmut Kohl

Sai dai wannan wasika ba ta kai ga Kohl ba saboda 'yan sanda masu farin kaya sun boye, saboda haka a cewar masanin tarihi Hans-Hermannn Hertle Kohl ko daya bai san cewa an kai wannan matakin ba. kamar yadda Egon Bahr mai baiwa shugaban gwamnati Willy Brandt shawara kan harkokin cikin Jamus da ketare ya bayyana

"Wannan abu ne da ban taba sanin zai yiwu ba, zan iya cewa a fahimta ta yadda muka yi aiki na tsawon makonni da watanni mu tabbatarda hakan, ya dai ce mu yi tambaya amma, ban taba tunanin wai zai kasance cewa karshen bangon Berlin abun da ke ufin karshen DDR ko kuma ma ba karo na farko ke nan da ya gana da wani kan wannan batu ba, ban taba sani ba."

Audioslideshow Helmut Kohl

Helmut Kohl da Walter Momper daga hagu lokacin jawabi a ofishin magajin gari a Berlin

A takaice dai daga taron na Walter Momper da Günter Schabowski da sauran mutanen, sun tsara cewa kafin a fara aiki da dokar shigi da ficin, za a yi fassfo wanda zai dauki makonni shida a kammala, sai dai bayan tattaunawa da rashin baci, ranar 9 ga watan Nuwamban, bai kamata a ce an yi sanarwar saukake zirga-zirgan ba domin an sanya mi shi takunkumi sai karfe hudu na safe lokacin da ya kamata a ce an sanar da jami'an kan iyaka, to amma saboda gajiyar da ya yi Günter Schabwoski daya daga cikin shugabanin yankin na DDR sai ya sanar cewa daga karfe bakwai dokar za ta fara aiki.

Shekaru da yawa bayan nan Schabowski bai mance da abunda ya faru lokacin taron manema labaran abu daya ne ke kan shi, mahukuntan Sobiet, bai ma ji tambayar da wani dan jarida ke mi shi ba na cewa ko dokar ta shafi wadanda ke zama a yammacin Berlin ba, amma abin da ya fi ba shi mamaki shi ne tun a shekara ta 1989 Jamusawa da kansu suka zartar da makomarsu da kansu.