Bikin sabuwar shekara cikin tsaro a Turai | Labarai | DW | 31.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin sabuwar shekara cikin tsaro a Turai

Kasashen yammacin duniya sun dauki kwararan matakan tsaro a daidai lokacin da al'ummomin kasashen ke tsaka da shagulgulan shiga sabuwar shekara ta 2016.

Mahukuntan Brussel na kasar Belgium sun yi nasarar cafke mutane shidda a ranar Alhamis, wadanda ake kyautata zaton suna yunkurin kawo barazanar tsaro a lokacin da ake tsaka da shagulgulan sabuwar shekara.

Kazalika kasar Faransa ma ta dauki irin wadannan kwararan matakan a wuraren shagulgulan bikin sabuwar shekarar a birin Paris. Ita kuwa Australiya ta samar da jami'an tsaro da dama don daukar kwararan matakan tsaro a birnin Sydney a lokacin wasan saki kayan wuta na sabuwar shekara ta 2016.