Bikin rantsar da shugaban kasar Afghanistan | Labarai | DW | 29.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin rantsar da shugaban kasar Afghanistan

A wannan Litinin din ce, akayi bikin rantsar da sabon Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani, wanda ya canji Shugaba Hamid Karzai da ke mulkin kasar tun 2001.

Tun dai da musalin karfe biyar da rabi ne agogon GMT aka fara shagulgullan rantsar da sabon shugaban a fadar shugaban kasar d ake birnin Kabul tare kuma da halartar manya-manyan baki daga kasashe da dama har ma da Shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain, da kuma babban abokin hamayyar sa Abdullah Abdullah dake a matsayin sabon shugaban gwamnatin kasar.

An dai kara tsaurara matakan tsaron a wannan kasa bisa tsoron da ake na 'yan Taliban suna iya amfani da wannan dama domin kai hari ga manyan baki da suka zo daga waje. Ranar Lahadi wani bam ya tarwatse a unguwar da ke da matakan tsaro a wannan birni, inda akasari nan ne ofishin jakadancin kasashe da dama suke. Ana iya cewa kasar ta Afghanistan dai na ci gaba da fuskantar matsalolin tashe-tashen hankula, musamman ganin yadda 'yan kungiyar Taliban suke kara kai samame a baya-bayan nan a yankin kudu maso yammacin birnin na Kabul wanda kuma hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo