1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar zaman lafiya a Jamhuriyar Niger

April 24, 2013

Yanzu dai zaman lafiya ya kankama a Jamhuriyar Niger, bayan shekaru masu yawa na yake-yake tsakanin gwamnatocin kasar da kungioyoyin yan tawaye na yankuna dabam dabam.

https://p.dw.com/p/18Mr2
Hoto: Bettina Rühl

A jamhuriyar Niger al'ummar kasar sun gudanar da sallar hadin kan yan kasa wacce gomnatin kasar ta assasa yau shekaru 17 da su ka gabata albarkacin kawo karshen yakin tawaye da kasar ta fuskanta shekaru da dama, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuwakn jama'a da kuma dukiyoyinsu.

Manya manyan rigingimun tawaye 4 ne kasar niger ta fuskanta a cikin kasa da shekaru 40 na baya bayannan. Daga ciki ukku 'ya'yan kabilar Abzinawa mazauna yankin arewacin kasar su ka tayar da su a shekara ta 1984 da ta 1991 da kuma shekara ta 2000, domin nuna rashin amincewarsu da abun da su ka kira ci da gumun al'ummominsu da gomnatoci ke yi ta hanyar kwasar arzikin karkashin kasa na Uranium da Allah ya huwacewa yankin nasu, amma kuma ba sa gani a kasa.

A yayin da a wajejen shekara ta 2000 'ya'yan kabilar Tubawa mazauna yankin gabacin kasar ta Niger suma su ka dauki makammai domin neman gomnatin ta kyuatata halin rayuwar al'ummomin yankin nasu. Ya zuwa yanzu dai dukkannin wasu ayyukan tawaye sun kawo karshe a kasar ta Niger a sakamakon yarjeniyoyi daban daban da gomnatin ta cimma da tsoffin kungiyoyin yan tawayen, musamman wacce aka cimma a shekara ta 1996 wacce gomnatin kasar ta Niger ta wancan lokaci ta kaddamar a matsayin ranar sallar hadin kan yan kasa. To sama da shekaru 15 bayan assasa wanann shiri ko minene matsayin tsaffin kungiyoyin yan tawayen Niger akan maganar hadin kan kasar? Mallam Rhissa Agbula shine ya wakilci kungiyoyin yan tawayen da su ka sanya hannu akan yarjejeniyar ajiye makamman a shekara ta 1996.

epa03142091 President
Shugaban jamhuriyar Niger Mahamadou IssoufouHoto: picture-alliance/dpa

Da ya ke tsokaci albarkacin wanann rana ta sallar hadin kan yan kasa PM kasar Niger Mallam Briji Rafini kira ya yi ga tsaffin kungiyoyin yan tawayen kasar ta Niger domin su hada kansu. To sai dai da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wannn batu na hadin kan kasa Dr. Sani Yahaya masani a fannin zaman takwar al'umma cewa ya yi idan Niger ta yi nasarar kawo karshen ayyukan tawaye to yanzu haka akwai wasu tabi'u wadanda musamman yan siyasa da yan boko ne ke yadasu a tsakanin al'umma da kuma ke yin barazana ga hadin kan yan kasar ta Niger a yau.

Kimanin kabilu 12 ne ke rayuwa kafa da kafada a kasar ta Niger, kuma masu lura da al'amurran yau da kullum na ganin babbar sa'ar da Niger din ta yi shine irin yanda kusan dukkannin kabilun 12 na da al'adun kusan iri daya, kuma addini daya na Musulunci sannan kuma akwai auratayya kusan a tsakaninsu su, abun da ke taimakawa wajan kara dankon zumunci da tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012
Pirayim Ministan Niger Briji Rafini ,Hoto: Getty Images

Mawallafi: Gazali Abdou Tassaoua
Edita: Umaru Aliyu