1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jarida a kasar Zimbabuwe na fuskantar matsaloli

Privilege Musvanhiri/SBMay 2, 2015

'Yan jarida a kasar Zimbabuwe na fuskantar matsalolin tafiyar da aiki daga gwamnati

https://p.dw.com/p/1FJ7g
Picture-Teaser Tag der Pressefreiheit
Hoto: Patrick Baz/AFP/Getty Images

Kasar Zimbabuwe kasar sauran kasashen duniya tana gudanar da bikin ranar 'yan jarida na duniya. A cikin wannan sharhi da Privilege Musvanhiri dan jarida daga kasar ta Zimbabuwe ya rubuta yadda gwamnatin take dakile yunkurin samun 'yancin kafafen watsa labarai.

Privilege Musvanhiri ya fara da cewa bayan kwashe shekaru 12 yana aikin jarida a Zimbabuwe ya yanke kaunar samun 'yancin 'yan jarida duk da cewa haka yana kunshe cikin sabon kundin tsarin mulki. Ya ci karo da matsaloli masu yawa. A wasu lokuka yana tunanin aikin jarida ya dace ya ci gaba ko kuma ya nemi wani zabin.

'Yancin 'yan jarida a Zimbabuwe na karkashin takura, kamar yadda aka yi alkawari an gabatar da dokoki na tsarin aiki bayan kwashe shekaru a cikin matsi, sai dai akwai tsaiko. Ana musgunawa tare da saka tarnaki ga 'yan jarida musamman wadanda suke aiki a kalilan din gidajen jaridu da ake wallafawa masu zaman kansu.

Simbabwe Symbolbild Pressefreiheit
Hoto: AFP/Getty Images/A. Joe

A karkshin dokokin kasar ta Zimbabuwe tilas dan jarida ya sabunta lasisin aiki duk shekara, wadanda ba su da asisi suna iya fuskantar daurin shekaru biyu a gidan fursuna.

Duk da haka 'yan jarida da suke da lasisi sau da yawa kan fuskanci cin zarafi daga hukumomi. Mahukuntan Zimbabuwe na nuna kyama musamman ga 'yan jarida masu daukan hoto.

A watan Satumba na shekara ta 2014 Musvanhiri da ya rubuta wannan sharhi ya sha duka a hannun jami'an tsaro masu lura da ababen hawa, saboda ya dauki hoto lokacin da jami'an suke takaddama da wani mai motar safa da ya karya dokokin hanya. Duk da cewa ya yi musu bayanin kan aikin da yake yi.

Privilege Musvanhiri
Privilege MusvanhiriHoto: Privilege Musvanhiri

Musvanhiri yana ganin 'yancin 'yan jarida shi ne gwamnati ta tabbatar da mutunta fadin albarcin baki tare da bai wa 'yan jarida kariya.

A shekara ta 2013 aka yi bikin samar da sabon kundin tsarin mulkin Zimbabuwe, wanda ya ba da tabbacin fadin albarkacin baki, tare da bai wa 'yan jarida kariya, amma ba haka lamarin yake a zahiri ba.

A watan Maris na shekara ta 2015 jami'ai daga kamfanin waya mai suna Econet Wireless sun yi dirar mikiya a jaridar harkokin kasuwanci The Source da ake wallafa a shafin Internet, domin neman wasu bayanai masu mahimmanci da suke zargin an sace daga kafanin.

Saboda halin ko'inkula na gwamnati ya janyo kara tabarbarewar halin 'yanci 'yan jarida a Zimbabuwe.

Idan aka yi maganar kariya ga 'yan jarida, ana fuskantar yanayin da ake tsare 'yan jarida ba tare da wata tuhuma ba. Ranar tara ga watan Maris wadanda ba a sani ba, sun sace dan jarida mai suna Itai Dzamara tun lokacin babu labarinsa. Dzamara ya sha sukar gwamnatin Shugaba Robert Mugabe. Lamarin ya girgiza 'yan jarida da dama, kuma haka ya kara dakile 'yancin fadin albarkacin baki.

Yanayin tattalin arzikin Zimbabuwe ya kara tabarbara aikin jarida. An rufe gidan jarida saboda kalubale. Haka ya zama kalubale ga 'yan jarida da iyalansu saboda hanyar samun kudaden shiga, sai dai ana fata wata rana a samu ci-gaba.