Bikin paɗakar da dunia a game da rikicin Darfur | Labarai | DW | 16.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin paɗakar da dunia a game da rikicin Darfur

Yau ne a sassa daban daban na dunia, a ka gudanar da biki karo na 4, na faɗakar da jama´a, a game da rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan.

A biranen London da Paris, ɗaruruwan jama´a su ka halarci zanga-zangar lumana, inda su ka gabatar da laccoci, masu kiran gwamnatin Sudan, ta bada haɗin kai, a yunƙurin warware wannan rikici.

Hukumar kare haƙƙoƙin jama´a ta Amnisty International, ta shirya bikin ta na faɗakarwa a harabar Tur Eifel da ke birnin Paris.

Ire-iren wannan shagulgula sun wakana a ƙasashen Amurika, Canada, Japon Mali, da dai sauran su ,inji Michel Luize kakakin hukumar Amnisty.

Ya bayyana wajibcin matsa lamba, ga gwamnatin Sudan, domin ta bada haɗin kai, ga ƙudurin Majlisar Ɗinkin Dunia na aika dakaru dubu 26 a wannan yanki.

Suma ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin jama´a, na Urgence Darfur da SOS Darfur sun gabatar da ƙasidoji ,masu kiran dunia ta dubi matsalar Darfur da idon rahama.