1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin nuna fina-fina na Berlinale a birnin Berlin

February 24, 2010

A ƙarshen makon da ya gabata a birnin Berlin hedkwatar tarayyar aka kawo ƙarshen bikin nuna fina-finai na ƙasa da ƙasa da aka fi sani da Berlinale.

https://p.dw.com/p/MAH4
´Yan wasan kwaikwayon na Amirka Leonardo DiCaprio da Michele Williams lokacin taro da manema labarai a wajen bikin BerlinaleHoto: AP

Bikin na bana dai shi ne karo na 60, kuma an mayar da hankali kan fina-finai na addinai da zamantakewa daga cikinsu kuwa da wani fim mai taken Shahada da wani daraktan shirya fina-finai ɗan Jamus mai asali da ƙasar Afghanistan wato Burhan Qurbani ya shirya. Fim ɗin dai ya ƙunshi wasu musulmai matasa su uku dake zaune a birnin Berlin waɗanda suka samu kansu cikin hali ƙaƙanikayi dangane da imani da kuma al´adunsu.

Fim ɗin dake ɗaya daga cikin fina-finan da aka nuna a lokacin bikin na Berlinale yayi ƙoƙarin nuna irin tasiri da kuma matsin lamba musamman da rayuwa a ƙasashen yamma ke yi akan rayuwa da zamantakewa ta musulmi mazauna a waɗannan ƙasashe. Hakazalika fim ɗin ya yi ƙoƙarin yin tsokaci kan ƙalubale na rayuwar musulmin zamani abin da ya kama daga kisan kare mutuncin gida har izuwa tsattsauran ra´ayin addini da kuma zaman ci-rani na ƙuncin rayuwa da wasu musulman ke samun kansu a ciki. A lokacin da yake amsa tambayoyi dangane da fim ɗin, Burhan Qurbani ya ce manufarsa ita ce kira da a shiga tattaunawa don ƙara samun fahimtar juna, sannan sai yayi ƙarin bayani kan dangantakarsa da addini.

Deutschland Film Berlinale Filmfestspiele 2010 Shahada
Tauraron ´yan wasa a fim ɗin ShahadaHoto: Berlinale 2010

“Da farko ina iya cewa gaskiya ni ba na bin dokokin musulunci sau da ƙafa. Amma ina kamantawa a rayuwata da kuma ma´amalata da sauran jama´a.  Abubuwan da aka gani a cikin fim ɗin ba dukkansu ne suka yi daidai da abubuwan dake faruwa a zahiri ba. Manufar ba ita ce mu yi wasan kwaikwayo game da zaman jama´a ko ainihin abubuwan dake faruwa a rayuwa ba. Abin da muka sa a gaba shi ne yin ƙarin bayani game da halin da wasu ciki da yin ƙoƙarin gano mafita. Wannan shi ne abin da muka mayar da hankali kai a cikin fim ɗin.”

Wani fim da aka mayar da hankali kai a lokacin bikin na Berlinale shi ne wani fim mai taken “Suna na Khan” dake nuni da zaman haƙuri da juriya. Mashahurin ɗan wasan kwaikwayo nan na ƙasar Indiya wato Shah Rukh Khan wanda ya fito a matsayin wani Ba-Indiye musulmi a Amirka bayan hare haren 11 ga watan Satumban shekara ta 2001. Shi dai wannan Ba-Indiye yayi fama da larurar taɓin hankali dake hana shi yin ma´amala da mutane. A lokacin da yake bayani game da fim din Khan cewa yayi manufarsa ita ce yiwa ´yan kallonsa bauta tare da sa su dariya.

“Duk wani addinin da muke maganarsa ko musulunci ko kiristanci ko yahudanci ko addini hindu, aƙidarsu ɗayar ce wato ɗa´a da biyayya. Su na nuna ma yadda za ka tafiyar da rayuwarka da samun kyakkyawan rabo. Dukkan addinan na na magana iri ɗaya wato ka so ɗan´uwanka mutum.”

My name is Khan Plakat
Allon tallar fim ɗin "My name is Khan".Hoto: picture alliance / dpa

Da ya juya kan masu amfani da addini don cimma wata manufa ta daban, musamman ma masu tsattsauran ra´ayi, Khan cewa yayi:

“Ina damuwa ina kuma firgita da kaɗuwa idan irin waɗannan abubuwan suka faru. Ba ni wata matsala ta saduwa da kowane irin mutum. Ina zantawa da su, ina sauraransu. In kan fada musu cewa wannan wasan kwaikwayo ne muke yi don nishaɗantarwa. Sadoda haka ku more, ku yi dariya. Ina fata wannan saƙon zai kai ga duk masu sha´awar kallon fim ɗi na.”

Wani fim da shi ma ya ja hankalin mutane a bikin na Berlinale shi ne na Feo Aladag haifaffiyar birnin Vienna na ƙasar Austriya mai taken Die Fremde wato Baƙi a harshen Hausa. Wannan fim dai ya nunar a fili saɓanin da ake samu tsakanin dokokin musulunci na al´ada da kuma na zamani. A fim ɗin dai wata Baturkiya matashiya ta yi ƙoƙarin gudu daga hannun mijinta da ya daɗe yana cin zarafinta. To amma ba ta samu goyon baya daga gidansu ba. Maimakon a ba ta kariya bayan ta tsere da ɗanta daga Istanbul zuwa Jamus sai iyayenta suka koma da ɗan wajen mijin. Ga furodusan fim ɗin dai wani ɓangare na matsalar ya shafi gazawar ƙasashen yamma kamar Jamus ta karɓar baƙi da hannu bibiyu daga ƙasashe kamar Turkiya.

“Me ke faruwa idan aka yi kisa na kare mutuncin gida? Idan ka dubi lamarin uba ko uwa ko kuma iyaye ne suke kashe ´ya´yansu. Hakan kuwa lalata makoma ne domin an halaka abin da ya kamata a kare shi. Ai al-Qur´ani mai tsarki ko littafin Bible ba su ce ka kashe ´ya´yanka ba. Saboda haka ina ganin ana amfani ne da addini a hanyar da ba ta dace ba don cimma wata manufa da babu ruwanta da addini."

Film Berlinale Son of Babylon
Tauraron da suka fito a fim ɗin "Son of Babylon."Hoto: Presse Kit

Ganin cewa addini ba ya nufin tashin hankali amma hanyar sulhu da sansantawa an ga haka a wani fim mai taken “Son of Babylon” da mai shirya fim Mohammed al-Daradji ya shirya. A fim ɗin wata dattijuwa ta yi balaguro da jikokinta daga arewacin Iraqi zuwa kudancin ƙasar, inda ta je neman mahaifin yara wanda tsohuwar gwamnatin Saddan Hussein ta yi awan gaba da shi. Mohammed al-Dadji na ganin fim ɗin a matsayin wata gudunmawa ta sake gina Iraqi.

“Matsalar mu a Iraqi ita ce ta rashin yafewa juna sai ɗaukar fansa. Yanzu al´adarmu ta fi dogaro kan ramuwar gayya, ba ma mai maganar yafiya. Saboda haka a wannan fim muka mayar da hankali kan yafiya. Idan da gaske muke wajen sake gina Iraqi to dole mu koyi yadda ake yafe laifi.”

Baya ga ´yan wasan kwaikwayo daga ko-ina cikin duniya bikin na Berlinale ya kuma samu halarcin shugabannin ´yan siyasa na ciki da wajen Jamus. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta ƙaddamar da bikin na bana ta yi nuni da cewa yanzu wannan dandalin ya zama wata cibiyar musayar al´adu.

“Berlinale bikin nuna fina-finai ne na ƙasa da ƙasa wanda ke muhimmanci. A yau wannan biki ya zama wani dandalin musayar al´adu. A halin da ake ciki fina-finai daga dukkan sassa na duniya kamar Asiya na samun karɓuwa a wannan biki. Berlinale ya zama tamkar maganaɗisun jan hankulan dubun dubatan ´yan kallo. Fina-finai wani ɓangare ne Tarayyar Jamus kuma wani ɓangare na manufofi raya al´adun mu.”

A bana fim ɗin da ya ci lambar yabo ta zinare shi ne na ´yan Turkiya mai taken Bal na Semih Kaplanoglu sai fim ɗin Roman Polanski mai taken Ghostwriter wanda ya samu lambar azurfa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar