Bikin ba da kyautar Nobel a Oslo da Stockholm | Labarai | DW | 10.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin ba da kyautar Nobel a Oslo da Stockholm

Shugaban hukumar dake kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, Mohammad Al-Baradei ya karbi kyautar zaman lafiya ta Nobel a bana a wani biki da aka yi a birnin Oslo. A cikin jawabinsa na godiya Al-Baradei ya dole ne a haramta makaman nukiliya a fadin duniya baki daya kamar yadda aka haramta cinikin bayi ko kisan kare dangi. Shugaban na hukumar IAEA ya ce ya zama wajibi a kawad da dukkan makaman nukiliya kimanin dubu 27 da ake da su a duniya. A kuma birnin Stockholm sarki Carl na 16 ya mika lambar yabo ga mutanen da suka ci kyautar Nobel a fannonin adabi, kiwon lafiya, tattalin arziki da kimiyar harhada magunguna.