1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matsin lamba ga Maroko kan alakarta da Isra'ila

December 13, 2020

Kungiyoyi da jam'iyyun da ke da nasaba da addinin Islama a Maroko sun yi watsi da tsarin Rabat wadanda a karkashin sa Shugaba Donald Trump na Amirka ya sasanta kasarsu da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/3me0S
Bildcombo I Benjamin Netanyahu ,Donald Trump, König Mohammed VI

Jam'iyoyin PJD da MUR sun hadu, sun fitar da wata sanarwar da ke cewa ba su amince da daidaita al'amurran diplomasiyya a tsakanin Maroko da Isra'ila ba, suna masu Allah-wadai da yunkurin cusa musu dabi'un Yahudawa a cikin al'ummarsu. 


Sai dai a  gefe guda rahotanni sun ce a karkashin sasancin da Amirka ta yi wa Maroko da Isra'ila, nan ba da jimawa ba za a fara karantar da tarihi da al'adun Yahudawa ga daliban ajin karshe na Furamare a Moroko. Kazalika hukumomin Isra'ila sun yi wa Marokon tayin sake bude ofishin jakadancinta da ta rufe a shekara ta 2000 a birnin Tel Aviv domin nuna goyon bayanta ga 'yancin Falasdinawa a wancan lokacin.