1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden: Trump na barazana ga dimukuradiyya

Abdul-raheem Hassan
September 2, 2022

Shugaba Joe Biden ya yi gargadin cewa ana cin zarafin dai-daito da dimukuradiyya a Amirka. Ya ce tsohon shugaban kasar Donald Trump da masu tsattsauran ra'ayi a jam'iyyar Republican suna barazana ga tushen kasar.

https://p.dw.com/p/4GLDR
Shugaban Amirka Joe Biden
Hoto: Matt Slocum/AP Photo/picture alliance

Joe Biden ya tuhumi Donald Trump da jiga-jigan magoya bayansa da hali irin na tsatstsauran ra'ayi da ke barazana ga harkokin siyasa da dimukuradiyyar Amirka, yana mai kira ga dukkan 'yan kasar su taimaka wajen dakile bara gurbi da ke cikin jam'iyyar Republican.

Da yake jawabi a zauren shelar ‘yancin Amirika a birnin Philadelphia na jihar Pennslavania, Shugaba Joe Biden yana cewa "Ba zan tsaya kallo ba, a soke nufin jama'ar Amirka ta makirci da hujjoji marasa tushe da da'awar zamba. Ba zan bari mutanen da suka yi yarda sun fadi zabe su saci kuri'u ba. Ba zan tsaya ina kallon mafi girman 'yanci a wannan kasa, 'yancin kada kuri'a da aka kirga a karbe su ba. A matsayina na shugaban ku, zan kare dimokuradiyyar mu da kowane zarafi na raina. Kuma ina rokon kowane Ba'amurke ya shiga tafiyar.