1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Amirka ya magantu da Benjamin Netanyahu

Abdoulaye Mamane Amadou
February 18, 2021

A karon farko Shugaba Joe Biden na Amirka ya tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, kan batutuwa da dama da suka shafi tsaro da batun nukuliyar Iran.

https://p.dw.com/p/3pW7b
Bildkombo Netanjahu und Joe Biden

A tattaunawarsu da Benjamin Netanyahu da ake yiwa kallon dan gaban goshin tsohon shugaban Amirka Donald Trump, sabon shugaban Amirka Joe Biden da Netanyahu, sun magantu kan rikicin Gabas ta Tsakiya da yarjejeniyar nukuliyar Iran, haka da batun yaki da annobar coronavirus.

Daukacin bangarorin dai sun nuna gamsuwa kan tattaunawar, tare da bayyana fatan ganin dorewar hulda a tsakaninsu, ko da yake rahotanni daga fadar shugaban Amirka, na cewar shugaba Biden ya bukaci ganin an samu dorewar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.