1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Biden na niyar kare masu auren jinsi

February 7, 2021

Shugaba Joe Biden na Amirka ya kaddamar da wani gangamin neman 'yanci mai karfin gaske ga masu auren jinsi a kasashen ketare, ya kuma sanya hakan a cikin manyan manufofin gwamnatinsa na hulda da kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/3p03j
Washington Außenministerium Rede USA Außenpolitik Biden
Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

Shugaba Biden ya kara kimar masu auren jinsin daga kan inda tsohon mai gidansa Shugaba Barack Obama ya tsaya, ya kuma sauya matsayi na ''ko in kula''  da gwamnatin Donald Trump ta sanya wa masu luwadi da madigo a cikin manufofin Amirka na ketare.

Tun a bayanin da Joe Biden ya yi game da manufofinsa na ketare ya ce yana son cikin kwanaki 180 hukumomin Amirka da ke aiki a ketare su kawo masa tsarin da za a iya amfani da shi wurin tallata 'yancin 'yan madigo da luwadi da kuma wadanda suka sauya jinsinsu, domin a ganinsa bai kamata a kyamaci kowa ba. 

Rahotanni sun ce biyo bayan hakan, sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken na shirin nada wakilin Amirka na musamman da zai rinka kula da hakkokin masu auren jinsi a kasashen duniya.