Biden ya ce babu guda babu ja da baya a tsayawa takara
July 12, 2024A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a karshen taron kungiyar tsaro ta NATO a Washington, Joe Biden ya ce yana burin kammala aikin da na fara a Amurka maimakon kare ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a baya. Shugaban ya kare kansa daga sukar da ake masa na cewar yakin neman zabensa na tafiyar hawainiya sakamakon alamun rashin koshin lafiya da tsufa da yake nunawa, inda ya shi ne wanda ya fi cancanta wajen tsayawa takara a karkashin Democrats a zaben Nuwanba mai zuwa.
Karin bayani: Biden da Trump sun yi fintinkau a "Super Tuesday"
Biden ya yi amfani da taron maneman labaran wajen bayyana cewar ba shi da dalilin yin magana da shugaban Rasha Vladimir Putin, amma ya sha alwashin ci gaba da goyon bayan Ukraine. Sannan shugaban na Amurka ya ce gwamnatinsa na samun ci gaba wajen cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Zirin Gaza.