1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bibiana Steinhaus ta kafa tarihi a Bundesliga

Suleiman Babayo
September 12, 2017

A ranar Lahadi ce (10.09.2017) aka kafa tarihi a gasar wasannin lig na Jamus da ake kira Bundesliga inda mace ta farko ta yi alkalancin wasan da aka kara tsakanin kungiyar Hertha Berlin da Werder Bremen.

https://p.dw.com/p/2jntO
Fussball Schiedsrichterin Bibiana Steinhaus
Bibiana Steinhaus mace ta farko da ta yi alkalanci a gasar BundesligaHoto: picture alliance/'dpa/M. Hitij

'Yar shekaru 38 da haihuwa jami'ar 'yar sanda, amma ta dade tana neman ganin yin abin da mahaifinta ya yi na alkalancin wasa. Ta yi alkalanci a wasannin cin kofin kwallon kafa na duniya na mata, da kuma wasannin Olympic, inda ta samu girmamawa daga takwarorinta maza, da masu horas da kungiyoyi gami da 'yan wasa, haka ya faru saboda yadda ba ta nuna sassauci ba.

Lokacin da Bibiana Steinhaus ta nuna katin gargadi ga daya daga cikin 'yan wasan. Kuma tana samun gagarumin goyon baya daga hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Jamus. Lutz Michael na a matsayin jagoran alkalan wasa na Jamus:

Steinhaus ta bai wa marada kunya

8. Bildergalerie erste Schiedsrichterin in der Geschichte der 1. Bundesliga
Bibiana Steinhaus tare da alakalan wasa 'yan uwanta na JamusHoto: picture-alliance/dpa/M. Balk

"Ina tsammani Bibiana ta kasance wani abu na musamman, saboda yanzu tana cikin Bundesliga. Wasan lig na Bundesliga yana da gagarumin tasiri a tsakanin kasashen duniya."

Ita dai Bibiana Steinhaus ba ta kasance bakuwa ba ga irin wannan yanayi. Ta dade tana fama da masu nuna tirjiya tsakanin jami'ai. Bibiana Steinhaus za ta gamu da 'yan gani-kashe-ni da ke goyon bayan kungiyoyin Bundesliga wadanda za su saka ido domin ganin hukuncin da za ta riga yankewa kan kungiyoyin da suke goyon baya, kuma babu sassaucin da za su nuna mata kan duk wani abu da suke gani bai yi musu dai-dai ba.