Benjamin Netayanhu ya kare kansa daga zargin cin hanci | Labarai | DW | 02.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Benjamin Netayanhu ya kare kansa daga zargin cin hanci

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kare kansa daga duk wani zargi da ake yi masa na karbar wasu kyatutuka na al'farma daga wasu shugabnnin kamfanoni.

Netanyahu ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai gabannin ammsa kiran 'yan sanda wadanda za su yi masa tanbayoyi game da zargin:''Na fada muku kuma na nanata babu abin da aka yi kuma babu abin da za a yi.''Ana zargin firaministan na Isra'ila da cewar  ya karbi gomai na miliyoyin daloli daga shugabannin kamfaoni da 'yan kwangila.