Benin: An kaddamar da sabuwar majalisa | Labarai | DW | 16.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Benin: An kaddamar da sabuwar majalisa

A jamhuriyar Benin an gudanar a wannan Alhamis a birnin Porto Novo da bikin kaddamar da sabbin 'yan majalisar dokokin kasar 83 da aka zaba a cikin wani yanayi mai cike da cecekuce. 

Sai dai bikin girka sabbin 'yan majalisar ya wakana ne a cikin tsauraran matakan tsaro inda gwamnatin kasar ta jibge tarin 'yan sanda da sojoji da ma motocin yaki a kewayen harabar majalisar dokokin baki daya. Kazalika gwamnatin ta girke jami'an tsaron nata da kayan yaki a wasu biranen da ke makobtaka da birnin na Porto Novo kamar Seme Podji.

Mutane akalla hudu ne dai suka rasa ransu a tarzomar da ta barke a zaben 'yan majalisar na ranar 28 ga watan Aprilu wanda 'yan adawar kasar ba su samu hurumin shiga ba. Illahirin 'yan majalisar 83 dai sun fito ne daga jam'iyyun da ke goyon bayan Shugaban kasar patrice Talon.