Bene ya rufta da ′yan makaranta a Legas | Labarai | DW | 13.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bene ya rufta da 'yan makaranta a Legas

An tabbatar da mutuwar 'yan makaranta 10 bayan faruwar lamarin, amma akwai fargabar samun karin asarar rayuka a hatsarin da ya faru a jihar Legas da ke Kudu mao yammacin Najeriya.

Gidan talabijin na Channels ta ce akwai makarantar firamare a saman benen da ya rushe kuma hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas da ta tabbatar da faruwar ibtil'in a yankin Itafaji da ke kusa da bakin ruwa ta ce ana cigaba da aikin ceto.

Ruftawar gini ya sha halaka mutane a Najeriya, inda kusan mutune 120 suka mutu a shekarar 2014 kawai sakamakon rushewar wani gini a jihar Legas.

A 2016 mutane 116 sun mutu bayan wani ginin coci ya rushe da su jihar, yayin da a shekarar 2016, wani gini da ba a kammala ba ya rufta inda nan ma mutane 34 suka rasa rayukansu, abin wasu ke dangantawa da rashin bin ka'idar yin gidi a kasar.