Beljiyam: Wanda ake zargi da kai hari ba shi aka kama ba | Labarai | DW | 23.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Beljiyam: Wanda ake zargi da kai hari ba shi aka kama ba

Jaridar ta La Libre Belgique ta ce mutumin da aka kama wani ne na daban sabanin wanda ta bada bayanan cewa an kama wato wanda ake zargi da kitsa harin na Brussels.

Belgien Terroranschläge in Brüssel Fahndung Verdächtige El Bakraoui

Daya cikin wadanda ake zargi da kitsa hari a Beljiyam

Kafafan yada labarai na kasar Beljiyam sun bayyana cewa rahoton da suka bayyana na cewa an kama mutumin da ake zargi da kitsa harin da aka yi a ranar Talata a filin tashi da saukar jiragen sama na Brussels da tashar jirgin kasa ba shi ne Najim Laachraoui ba.

Jaridar ta La Libre Belgique ta ce mutumin da aka kama wani ne na dabam. Ita ma jaridar DH da ta bada rahoton da fari, ta ce mutumin da aka kama a lardin Anderlecht ba shi ba ne wanda ake zargi da kitsa harin.

'Yan sanda dai da masu gabatar da kara sun ki cewa komai ga me da wannan batu sai dai nan gaba da ranar nan zasu yi karin bayani.