Beljiyam ta lallasa Ingila da ci 2:0 | Labarai | DW | 14.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Beljiyam ta lallasa Ingila da ci 2:0

A karon farko a tarihi Beljiyam ta samu matsayi na uku a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya bayan da ta doke Ingila da ci biyu da nema a gasar da aka buga a filin wasa na Saint Petersburg.

FIFA WM 2018 Belgien gegen England (Reuters/D. Martinez)

Thomas Meunier dan wasan Beljiyam na murnar samun nasara

Beljiyam ta lallasa Ingila da ci biyu da nema domin samun matsayi na uku a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

Ana fara wannan wasa cikin mintoci hudu na farko dan wasan kasar Beljiyam mai suna Thomas Meunier ya jefa kwallo na farko a ragar Ingila.

Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Beljiyam ta samu wannan matsayi na uku, domin ta sha kashi a hannun Faransa a shekarar 1986 lokacin neman matsayin na uku a wasan da ya wakana a kasar Mexiko, wanda Argentina ta dauki kofi bayan doke Jamus a wasan karshe. Yayin da ita Ingila ta taba lashe kofin sau daya a shekarar 1966 lokacin da ta shirya gasar.

A gobe Lahadi ake kawo karshen gasar ta neman cin kofin kwallon kafa ta duniya, inda za a fafata tsakanin Faransa da Croatia a filin wasa na Luzhniki dake birnin Moscow.