Beljiyam: Gidan adana kayan tarihin Afirka | Zamantakewa | DW | 15.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Beljiyam: Gidan adana kayan tarihin Afirka

Bayan aikin gyara na sake masa fasali na tsawon shekaru biyar, a kwanakin baya an yi bikin sake bude gidan adana kayayyakin tarihin Afirka da ke kasar Beljiyam.

Leopold II König von Belgien (picture-alliance/dpa/Glasshouse Images)

Sarki Leopold II da ya jagoranci mulkin mallakar da Beljiyam ta yi

Tun ba yau ba ake wa gidan kallon wani wurin yada farfagandar iyalan gidan masarautar Beljiyam a kan mulkin mallakar da suka yi wa Kwango. Wasu 'yan asalin Afirka a kasar ta Belgium ba su gamsu da sabon yunkurin na kwaskware irin sakon da gidan tarihin ke aike wa jama'a ba. A wani katafaren fili da ke a wajen Brussels, kasar Beljiyam na kokarin yin amfani da gidan adana kayayakin tarihin na Afirka da aka yi wa garambawul, domin wanke kanta daga tabon mulkin mallaka na rashin imani da ta yi wa Kwango. Sai dai wasu sun ce filin a gurbace yake har abada, bisa tuni da abubuwan da suka wakana a da. Koekie Claessens daya ce daga cikin daraktocin aikin sake fasalta gidan tarihin, ta nuna wani yanki da ke wajen gidan tarihin da ke tuni da yadda wurin ya kasance a shekarar 1897 lokacin da Sarki Leopold na biyu, da a yanzu aka kyamace shi saboda ta'asar da ya aikata a Kwango, ya samar da wannan fada ta farfaganda da ta sha ado da gwala-gwalai da sauran kaya masu daraja da aka sato daga Afirka da wasu hotuna masu kaskantar da Afirka har ma da wani gidan dabbobi wato zoo na dan Adam.

Königliches Museum für Zentralafrika in Tervuren (DW/T. Schultz)

Gidan adana kayan tarihin mulkin mallakar da Beljiyam ta yi a Afirka

Daga cikin rubuce-rubuce na neman gafara da gidan kayan tarihin ya yi, har da sunayensu da aka rubuta kan bango da kuma sunayen 'yan Beljiyam fiye da 1500 da suka mutu lokacin mulkin mallakar. Koekie Claessens ta ce matakin da gidan tarihin ya dauka na duba wancan lokacin, abu ne mai sosa rai. Sai dai akwai abubuwa da dama game da gidan tarihin wanda kafin a yi masa gyara wasu ke kiransa "gidan tarihin mulkin mallaka na karshe a duniya" musamman saboda rashin kaucewa daga ainihin manufar Sarki Leopold na biyu dangane da galabar da ya samu a Kwango. An dai kiyasta ya halaka mutane kimanin miliyan 10. Daraktan gidan tarihin Guido Gryseel ya yi bayanin yadda 'yan Beljiyamke jan kafa wajen amsa cewa mulkin da Sarki Leopold ya yi a Kwango, ya kassara kasar domin arzurta kasarsa wato Beljiyam. Gryseel ya ce ra'ayinsu a yanzu shi ne mulkin mallaka a matsayin tsari na shugabanci babban kuskure ne. Ya ce za a samu ra'ayi mabambanta daga maziyarta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin