1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayern Munich ta zamo zakara a Bundesliga

Gazali Abdou Tasawa
June 17, 2020

Kungiyar Bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga ta shekarar bana bayan da a yammacin jiya Talata ta doke Breen da ci daya da babu a wasannin mako na 32.

https://p.dw.com/p/3dton
1. Bundesliga | FC Bayern Meisterschaft | Jubel
Hoto: Getty Images/S. Franklin

Kungiyar bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga ta shekarar bana bayan da a yammacin jiya ta doke kungiyar Bremen da ci daya da babu a wasan mako na 32. 

Yaya babba Bayern Munich ta lashe gasar ta Bundesliga ne bayan da a yanzu haka take da maki 76, wato tazarar maki 10 tsakaninta da yaya karama Borussia Dortmund a lokacin da ya rage wasanni uku a kammala gasar wanda ke nufin ba za a iya kamota ba ko da ta baras da sauran wasanninta uku.

Wannan dai shi ne karo na 30 kuma na takwas a jere da kungiyar ta Bayern Munich ke zama zakarar wasannin kwallon kafar kasar ta Jamus na Bundesliga.