1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayani kan cutar kuturta da makanta

May 14, 2014

Tambaya ta fito ne daga Rilwan Tijani Askira a Najeriya, inda yake son sanin ko me ke kawo cutar makanta da kuturta, kuma ko ana gadon su...

https://p.dw.com/p/1BzY1
Kenia Blinde in Afrika
Hoto: DW

To filin na amsoshin tambayoyin ku, ya samu tataunawa da kwararren likitan idanu a babban asibitin birnin Damagaram na jamhuriyar Nijar Docta Ba'are Ibrahim inda ya fara da cewa...

Abubuwa da dama ne ke haddasa cutar makanta, domin akwai cututtuka da dama da ake kamuwa da su na idanu wadanda idan ba a dauki matakai a kansu ba, sukan iya kaiwa ga makanta. Musali kamar a kasar Nijar, a jihar Damagaram akwai cutar ciwon idon amadari da al'umma ke fama da ita, wadda idan aka dauki matakai tun da wuri, to ba ba za ta kai ga makanta ba, sannan kuma akwai cutuka da su kuma suka danganci tsufa, wandanda idan mutun ya tsufa, to akwai wasu jijiyoyin idanu da suke saki, inda har ake samun cutar yanar idanu, kuma banda haka, akwai ta hanyar jin rauni a idanu, da dai sauran su duk suna iya haddasa makanta.

An Flussblindheit erkrankter Afrikaner
Hoto: AP

Sannan kuma akwai makanta da ake iya gado daga uwa ko daga uba, wandda kwayar cutar na jikin uwa ko uba dan haka, idan ba'a dauki wasu matakai ba a fannin likita, to yayan su na iya daukan wannan cuta, dan haka ta wani fannin ana gadon cutar makanta.

Bisa abun da ya shafi cutar kuturta kuwa, Docta Bouzou Sawidi, likitan dake kula da harkar Kuturta da babban tari, a babban asibitin birnin Damagaram ya bada haske, inda yake cewa....

Lepra in Indien
Hoto: AFP/Getty Images

Abun dake kawo cutar kuturta wata kwayar cuta ce da ake kira (Bacille) da harshen Faransanci, wanda wani masanin kimiya da ake kira Hensin ne, ya gano shi a shekarar 1873, harma ake kiran kwayar cutar Bacille de Hensin da Faransanci. Ita dai cutar kuturta cuta ce da ta shafi fatar jiki a karon farko, kafin daga bisani ta kama jijiyoyi, kuma cuta ce da ba'a gadon ta, amma ana iya samun ta daga wanda yake dauke da ita, idan akwai mu'amala mai yawa tskanin su, amma kuma a cewar Likita idan kuma mai dauke da kwayar cutar na shan magani, to ana iya rayuwa dashi ba tare da an dauki wannan cuta ba.

Domin a cewar likita duk wanda ya ga alamun cutar ya yi sauri ya je asibiti, to akwai magunguna da ake bayarwa kuma mai cutar na iya warkewa tun kafin ta kai ga kama jijiyoyinsa, ma'ana tun kafin ta kai ga makantarwa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal