Batun tsaro da tattalin arziki sun mamaye taron AU | BATUTUWA | DW | 04.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Batun tsaro da tattalin arziki sun mamaye taron AU

Taron koli na Kungiyar Kasashen Afirka ta AU da ya gudana a birnin Addis Ababa ya tattauna tare da daukar matakai kan batutuwa da suka shafi tsaro da tattalin arziki da na 'yan gudun hijira da sauran matsaloli.

Shugaban kwamitin gudanarwa na Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki da ya jagoranci taron ya zano jerin kalubale da ake fuskanta a cikin kasashen nahiyar wadanda suke jiran amsa daga kungiyar ta Tarayyar Afirka inda ya ce ''tsaro na ci gaba da ci mana tuwo a kwarya, idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a kasashe kamar su Sudan ta Kudu da Somaliya da Libiya da a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Tabarbarewar huldar dangantaka tsakanin Djibouti da Eritriya da ma yadda 'yan ta'adda ke kara bunkasa na zaman babban kalubale da Afirka ke fuskanta.''

Sansibar Wahlen Jugendliche Anhänger CUF (DW/M. Khelef)

Batun karuwar al'umma a Afirka musamman matasa na daga cikin abinda taron AU ya tattauna a kai

Taron kolin kungiyar Tarayyar Afirkar ya kuma tattauna batun saurin yaduwar al'ummar Afirka wacce daga mutun miliyan 100 a shekara ta 1900 ta kai adadin mutun miliyan 1200 a shekara ta 2016. Alkalumman sun nunar da cewa idan aka tafiya haka 'yawan al'ummar Afirkar zai kai kusan mutun miliyan 4500 a shekara ta 2100. Wannan ce ta sanya batun inganta makomar matasan Afirka ya kasance a sahun gaban na batutuwan da taron kolin kungiar ta AU ya tattauna a kai. Alkalumman kididdiga sun nunar da cewa kashi 70 daga cikin dari na al'ummar Afirka matasa ne. A kan haka ne ma sarkin Maroko Mohammed na shida ya bayar da shawarar ganin kasashen Afirka sun dauki matakin bai daya na yaki da matsalar kwararra da matasan zuwa nahiyar Turai.

29th African Union Summit (African Union Summit picture alliance / AA)

Mugabe ya bada misali na samawa Kungiyar AU kudin shiga inda ya bada tallafi na euro kusan miliyan guda

Taron har wa yau ya kuma tattauna fito da hanyoyin samar da kudaden gudanarwa na Kungiyar ta yadda za ta daina dogaro da kasashen ketare. A kan haka ne mahalartansa suka jaddada bukatar aiwatar da shirin kafa wani haraji na musamman kan hajojin da ake shigo da su daga wajen zuwa cikin kasashen na Afirka kamar dai yadda Shugaba Ouattara Alassane ya bayyana sai dai wasu masu fafutuka na adawa da wannan batu. Game da batun samar da kudaden shiga shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya bayar da kyakyawan misali inda ya sayar da shannunsa guda 300 da suka bashi damar samun kudi tsaba euro dubu 879 wadanda ya tallafawa kungiyar da su.

Sauti da bidiyo akan labarin