Batun nukiliyar Iran na fuskantar turjiya | Siyasa | DW | 24.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Batun nukiliyar Iran na fuskantar turjiya

Tattaunawar nukiliyar Iran da ta gudana a birnin Vienna ta watse ba tare da cimma yarjejeniya ba, amma kuma mahalarta taron sun sake daukan wa'adi ya zuwa 30 ga watan Yuni na 2015.

Batun da har yanzu ke kawo cikas a tattaunawar tsakanin Iran da kasashen nan biyar masu kujerun dindindin a Majalisar Dinkin Duniya hade da Tarayyar Jamus, shi ne lokacin da za a dage takunkuman da aka kakaba wa Iran da kuma rage yawan sinadaranta a shirinta na nukiliya. James Phillips na gidauniyar The Heritage Foundation da ke birnin Washington, kuma masanin harkokin yankin gabas ta tsakiya, ya ce tattaunawar ba batun zaman lafiyar Amirka ka dai ta shafa ba.

"Amirka na da muradunta na tsaro. Ba ma kawai na ta kadai ba har da na kawayenta, musamman na yankin gabas ta tsakiya kamar isra'ila da Saudiyya da kuma kasashen yankin Golf, wadanda ke cikin hadari saboda karfin dakarun Iran. Idan wadannan dakaru suka samu makaman nukiliya, ai batu ya baci."

Tun a farkon wannan shekara wakilan Democrats 15 a majalisar dattawan Amirka, suka sanya hannu kan wata bukatar tsawaita takunkumai kan Iran, amma kasancewa a lokacin Demokrat din ce ke da rinjaye a majalisar shugabanta Harry Reid ya hana a kada kuri'a kan wannan bukata. Sai dai bayan zaben 'yan majalisun na kwanan nan abubuwa sun canja wa shugaba Barack Obama, inda yanzu haka sabon shugaban majalisar dattawan ya goyi bayan tsananta jerin takunkumin. Shin ko Obama zai yi nasarar shawo kan masu rinjayen yanzu a majalisun dokokin? Jim Walsh na jami'ar MIT ya nuna tababarsa.

"Daya bangaren zai yi adawa da kowane mataki Obama ya dauka. Za su yi kokarin rusa duk wata yarjejeniya da Iran. Akwai kuma wani bangare da ya damu da abin da ka iya faruwa. Ba su yarda da Iran ba saboda matsaloli masu yawa da aka fuskanta da kasar a shekarun baya. Saboda haka ba za a samu wata yarjejeniya kyakkyawa ba. A da ma ba wata kyakkyawar yarjejeniya a duniya"

Obama na son kawo karshen takaddamar da aka kwashe shekaru masu yawa ana yi da Iran sannan yana son shawo kan gwamnatin Teheran ta zama kawar Amirka a kan batun tsaro a yankin gabas ta tsakiya musamman wajen yaki da 'yan ta'addan kungiyar IS da ke fafatukar kafa daular Musulunci a Iraqi da kuma Siriya.

Sauti da bidiyo akan labarin