Batun nukiliyar Iran da wasu kasashen Turai | Siyasa | DW | 11.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Batun nukiliyar Iran da wasu kasashen Turai

A yi sabon zama tsakanin kasar Iran da kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya gami da kantomar harkokin wajen Kungiyar Tarayyar Turai ta EU kan yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar Iran.

Iran Teheran Treffen zwischen dem Iran und der EU (Ilna/A. Ramezani)

Haduwa tsakanin wasu kasashen Tarayyar Turai da Iran

 

Gabanin fara wannan tattaunawa dai Kungiyar EU ta ce ta nan kan matsayin da ta dauka na amincewa da yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar Iran wanda ya tanadi gudanar da shi kacokan kan samar da makamashi maimakon yunkuri na samar da makaman kare dangi, wannan ne ma ya sanya mambobin kungiyar neman dukannin wanda ke da ruwa da tsaki kan sha'anin da su mutunta tanade-tanaden da yarjejeniyar ta yi. Sigmar Gabriel shi ne ministan harkokin wajen Jamus, ya shaidawa DW cewa baya ga kasarsa, wasu karin kasashe da ke da karfin fada a ji a Turai na kan godabe guda da Jamus.

USA Außenminister Gabriel in Washington (picture-alliance/dpa/G. Fischer)

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Sigmar Gabriel

"Da mu da Iran mun amince kan yarjejeniyar da aka cimma game da shirinta na nukiliya. Mun amince kan Tehran ta dakatar da shirinta na nukiliya sannan ta inganta harkokinta na tattalin arziki da na rayuwar al'umma. Da EU da Birtaniya da Faransa wanda hakan ba zai amfana wa kowa komai ba."

Wadannan kalamai da Gabriel ke yi ba za su rasa nasaba da tunanin da ake da shi na yiwuwar sake kakabawa Iran din takunkumi ba daga bangaren Amirka don kuwa a ranar Juma'a 12 ga wannan wata na Disamba ne Shugaba Donald Trump zai dauki mataki kan sanya takunkumi ko akasin haka ga kasar ta Iran. A baya dai Trump ya sha bayyana cewar yarjejeniyar da aka cimma ba ta kan ka'ida kana ita ce irinta mafi muni da Amirka ta sanya hannu a kai. Sai dai Sascha Lohmann wanda masani ne da ke jami'ar Havard a Amirka ya ce kafin a kai ga sanya wa Iran takunkumi dama tana da tarin matsaloli wanda ta haifar da kanta.

Brüssel Iran EU Treffen Federica Mogherini Jean-Yves Le Drian (Reuters/J.Thys)

Kantomar kula da harkokin waje ta Tarayyar Turai Federica Mogherini da Jean Yves Le Drian ministan harkokin wajen kasar Faransa

"Galibin matsalar tattalin arzikin Iran a cikin gida aka kirkireta ko da dayake idan aka duba ta wata fuskar za a iya cewa mayar da ita saniyar ware da kasashen duniya da manyan kamfanoni da bankuna suka yi ya taimaka wajen jawo matsalar."

Yanzu haka dai al'ummar Iran da ma ta sauran kasashen duniya na zuba idanu don ganin irin yadda za ta kaya game da matakin da ShugabaTrump na Amirka zai dauka kan Iran din da matsayar da za a dauka bayan kammala taro na tsakanin Iran da wasu kasashen EU kan yarjejeniyar da aka rigaya aka cimma kan shirin nata na nukiliya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin