Batun kafa gwamnatin hadaka a Jamus | BATUTUWA | DW | 31.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Batun kafa gwamnatin hadaka a Jamus

Manyan jam'iyyun siyasar Jamus da ke tattauna batun kafa gwamnatin kawance da nufin kawo karshen dambarwar siyasa ta tsawon watanni hudu, sun cimma dai-daito a daya daga cikin muhimman batutuwa.

Deutschland Merkel, Seehofer und Gabriel ARCHIV (picture alliance/dpa/M. Gambarini)

Angela Merkel da Sigmar Gabriel na jam'iyyar SPD kuma ministan tatalin arziki na Jamus da kuma Horst Seehofer shugaban jam'iyyar CSU

Batun 'yan gudun hijira musamman ma dai wanda ya shafi sake hadewar iyalansu sune muhimmai a tattaunawar kafa gwamnatin kawance tsakanin jam'iyyun CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kawarta ta CSU da kuma jam'iyyar masu ra'ayin gurguzu ta SPD karkashin jagorancin Martin Schulz. A ci gaba da zaman tattaunawar, jam'iyyun sun amince kan batun mai sarkakiya wanda kuma ke kawo cikas a kokarin kafa gwamnatin kawance a tarayyar ta Jamus. Za a dakatar da yarjeniyar da aka bullo da ita a 2016 dangane da hadewar iyalan na 'yan gudun hijira da ke son kawo danginsu Jamus har zuwa ranar 31 ga watan Yuli, sannan daga ranar 1 ga watan Agusta za a yarda iyalai har dubu daya su shigo Jamus su zauna da 'yan uwansu da aka ba wa mafaka amma da izini na zama a kasar tsahon shekara guda kacal, ko da yake za a iya tsawaita shi

Syrische Flüchtlingsfamilie in Ägpyten und Deutschland (Lana Hamoush)

Wasu iyalai daga Siriya da suka rabu biyu, rabi a Masar rabi kuma a Jamus

Jam'iyyun sun kalli lamarin ta fuskoki mabambanta.

Sai dai jim kadan bayan sanarwar cimma yarjejeniya kan batun, wakilan jam'iyyun sun gabatar da fassarori mabambanta ga ka'idojin yarjejeniyar. Volker Bouffier da ke zama mukaddashin shugaban jam'iyyar CDU ya ce har yanzu akwai abubuwa masu daure kai a yarjejeniyar yana mai cewa: "Batun abin da za a iya karawa wato abin nufi yadda za a tunkari wadanda lamarinsu ke da sarkakiya ake kuma da shakku a kai, to har yanzu batu ne da ake takaddama a kansa, wanda kuma har yanzu muke tsakiyar tattaunawa a kai."

Jam'iyyar CSU da ke zama babbar kawar jam'iyyar CDU tana da shakku kan batun a cewar kakakinta na majalisar dokoki Alexander Dobrindt: "Da ma ka'idar tana da tsauri, za ta kuma ci gaba da zama a haka. Ba za a tsawaita lokacin ba ko samar da sabuwar ka'ida musamman dangane da 'yan gudun hijira da lamarinsu ke da sarkakiya."

 

Har yanzu akwai sauran rina a kaba


Koalitionsverhandlungen zwischen Union und SPD (Getty Images/AFP/O. Andersen)

Shugaban jam'iyyar SPD Martin Schulz

Ita kuwa a nata bangaren jam'iyyar SPD a ta bakin shugabar gungun wakilanta a majalisar dokoki, Andrea Nahles cewa ta yi ba bu wata yarjejeniya ta ci gaba da wannan batu. "Tun da can ma akwai ka'aidar ta 'yan gudun hijirar da lamarinsu ke da sarkakiya. Amma gaskiya ba mu cimma wata yarjejeniya ba bayan doguwar tattaunawar da muka yi cewa muna da bukatar tsawaita wannan batu. Sai dai yanzu za mu gaggauta kafa wata doka da za ta share hanyar shigo da iyalai dubu 12 karkashin tarin sake hadewar iyali." Sai dai shugaban bangaren matasa na SPD Kevin Kühnert da ke jagorantar wani kamfe a cikin jam'iyyar na adawa da kulla kawance da Merkel wanda kuma har wa yau ke kira da a saukaka ka'idojin ba da mafaka, ya ce bai gamsu da wannan yarjejeniyar ba. Amma shugaban SPD din Martin Schulz ya yaba da yarjejeniyar yana mai cewa ya yi nasara a kan masu ra'ayin mazan jiya, abin da ke nufi fiye da 'yan gudun hijira dubu daya za su rika samun izinin shigowa Jamus a kowane wata karkashin tsarin musamman na 'yan gudun hijira da lamarinsu ke da sarkakiya.

Sauti da bidiyo akan labarin