Batun Boko Haram ya mamaye taron AU | Siyasa | DW | 30.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Batun Boko Haram ya mamaye taron AU

Batun rikicin Boko Haram da kuma Ebola ne suka mamaye taron shugabannin kungiyar kasashen Afirka AU karo na 24 da ke gudana a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.

Taken taron na bana dai shine "Shekarar samawa mata abin dogaro da kai da ci gaban Afirka nan da shekara ta 2063." Sai dai maimakon taron ya duba matsalolin da ke addabar matan da kuma wanda suka hana nahiyar Afirkan ci gaba, baki daya hankulan mahalarta taron ya raja'a ne a kan batun tashe-tashen hankula na kungiyar Boko Haram da ta addabi Tarayyar Najeriya da ma sauran kasashen da ke makwabtaka da ita. A jawabin da tayi, shugabar hukumar kungiyar hadin kan kasashen Afirkan wato AU Nkosazana Dlamini Zuma, ta ce barazanar da kungiyar Boko Haram din ke yi na bazuwa zuwa sauran kasashen nahiyar tana mai cewa.

Bazuwar Boko Haram a wasu kasashe

"Cin zarafin da kungiyar Boko Haramke yi a kan al'ummarmu ta hanyar yin kisan wulakanci da lalata dukiyar al'umma da sacewa tare da yin ikirarin sayar da mutane musamman ma kananan yara mata ta hanyar sace su da kuma aurar dasu da kai hare-haren ta'addanci a kauyuka, babbar barazana ce ga fannin tsaronmu da ci gabanmu baki daya."

Boko Haram

Boko Haram

A jawabinsa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon da shima ke halaratar taron na AU cewa ya yi cin zarafin da Boko Haram ke yi na haifar da gagarumar barazana ga bangaren tsaro na kasashen nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

"Ayyukan ta'addanci basu da iyaka, kuma suna shafar kasashen Afirka a yankin Sahel da ma sauran gurare."

Kungiyar ta AU dai na bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wani asusu da zai taimakawa rundunar hadin gwiwa da kungiyar za ta tura Najeriyar wadda ta kunshi dakaru 7,500 daga kasashe biyar, ta fuskar kayan aiki da kudade. A kalla mutane 13,000 ne suka hallaka a Najeriyar daga shekara ta 2009 kawo yanzu sakamakon hare-haren na Boko Haram.

Najeriya na maraba da rundunar hadin gwaiwa

Sabon shugaban kungiyar AU Robert Mugabe

Sabon shugaban kungiyar AU Robert Mugabe

A baya rahotanni sun nunar da cewa Najeriyar ta ce bata maraba da duk wani taimako da za a bata daga kasashen ketare, sai dai a hirarsa da tashar DW kakakin fadar gwamnatin Tarayyar Najeriyar Reubin Abati wanda ya ce sunyi maraba da matakin, ya musanta wannan zargi yana mai cewa...

"Najeriya ba ta taba nuna kin amincewa da hada kai da kasashen da ke makwabtaka da ita ba wajen yakar Boko Haram, a koda yaushe shugaban kasa Goodluck Jonathan na cewa ana bukara taimako daga kasashen yankin dama na duniya baki daya."

A na sa ran taron na kungiyar ta AU zai kuma tabo batun rikicin Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da kuma annobar cutar Ebola mai saurin kisa da ta addabi wasu kasashe na yankin yammacin Afirka da kafa wani asusun tallafawa kasashen da bala'in Ebolan ya yi kamari domin farfado da tattalin arzikinsu da kuma kafa cibiyar kula da cututtuka ta Afirka. A hannu guda kuma kungiyar ta AU ta zabi shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe a matsayin sabon shugaban kungiyar wanda zai ja ragamar AU din nan da shekara guda mai zuwa, inda ya karbi shugaban kasar Moritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz. A jawabin da ya yi na maraba yayin taron Mugabe da ya yi kaurin suna wajen rikici da kasashen yamma, ya ce albarkatun Afirka na Afirka ne ba na kowa ba sai abokai da Afirkan ta gayyota amma ba 'yan mulkin mallaka ba.

Sauti da bidiyo akan labarin