1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barrow na shirin zarcewa a karo na biyu

December 4, 2021

Tuni dai Shugaba Adama Barrow ya bayyana kwarin gwiwar iya lashe zaben shugaban kasar ta Gambiya da ya gudana a wannan Asabar din.

https://p.dw.com/p/43pwZ
Gambia | Präsidentschaftswahlen in Banjul | Präsident Adama Barrow
Hoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance

 

Kwarya kwaryar sakamako da hukumar zaben Gambiya ta fitar a yau Lahadi na nuna cewa shugaban kasar Adama Barrow na samun nasara da gagarumin rinjaye yayin da ake ci gaba da kirga kuri'u. Kawo yanzu dai jam'iyya mai mulki a kasar ta NNP na kan gaba a mazabu 40 cikin 53 da ake da su.

Tuni dai dama shugaba Barrow ya ke da yakinin yin ta-zarce a karo na biyu bayan samun nasara kan tsohon shugaban Gambiya Yahya Jameh da ake yi wa kallon wanda ya yi mulkin kama-karya. Ana dai sa ran sanar da sakamakon zaben kafin nan da wayewar garin gobe Litinin.

Zaben dai zai kasance na gwajin nasarar dimukuradiyya a Gambiya. Jam'iyyu biyar ne dai ke fafatawa a zaben na shugaban kasa.