Barazanar yunwa a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 29.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar yunwa a Sudan ta Kudu

Matsalar yunwa a Sudan ta Kudu ta kai wani matsayi mafi girma inda a halin yanzu kayayyakin masarufi suka yi tsada.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da abinci ta FAO ce dai cikin wata sanarwa ta ce abubuwan da suka yi saura na abinci ya zuwa karshen wannan shekara a kasar ba su taka kara suka karya ba, sannan kuma ana fuskantar saurin karewar kayayyakin abincin da kuma matsanancin tsada.

Har kawo yanzu dai ana ci gaba da gwabza fada tsakanin bangarorin kasar ta Sudan ta Kudu duk kuwa da yarjejeniyar da aka cimma a watan Augusta da ya gabata. A karo da dama dai masana harkokin abinci sun sanar cewa yankunan jihar Unity ta Arewa na daf da fadawa cikin halin matsananciyar yunwa a kasar ta Sudan ta Kudu.