1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mosambik: 'Yan ta'adda na barazana

Antonio Cascais, ATB/LMJ
August 20, 2020

Mayaka masu ikrarin jihadi Mozambik, sun sha kai hare hare da ma kwace birnin Mocimboa da Praia. Koda yake tashar jirgin ruwan da ke birnin na, ba a dauke ta a matsayin mafi muhimmanci a arewacin kasar ba.

https://p.dw.com/p/3hGUH
Mosambik Valigy Tauabo
Valigy Tauabo gwamnan birnin Cabo Delgado da aka kai harin ta'addanci a MosambikHoto: DW/D. Anacleto

Manazarta dai na ganin cewa karbe tashar jirgin ruwan ta birnin Mocimboa da Praia, babban abin kunya ne ga sojojin gwamnatin Mozambik. Abdullahi Tanko Bala na dauke da karin bayani. Birane kamar Mocimboa da Praia da sauransu sun kasance tamkar inda aka yi yakin basasa a cewar 'yar jarida mai bincike Estacio Valoi wadda ke aike wa mujallar "Moz 24 Horas" rahotanni daga yankin. 

Bayan hare haren farko da suka auku a yankin a watan Oktoban 2017, an kone kauyuka da dama kurumus. An hallaka mutane da dama tare  da tagaiyara wasu a cewar 'yar jarida Estacia Valoi: "Tun makon da ya wuce, a ranar Asabar da kuma Litinin, hare haren sun tsananta, a cewar sojoji da kuma wasu majiyoyi. Lamarin dai gaba daya ya yi kamari kuma ya kare da 'yan ta'adda da suka karbe iko da Mocimboa da tashar jirgin ruwan."
A 'yan kwanakin da suka wuce iyalai da dama sun tsere ta jiragen kwale-kwale wasu kuma a kananan motocin kirar bus zuwa Pemba babban birnin Cabo Delgados. Lamarin ya ta'azzara ko ma a ce ya gagari kundila. Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun ce, mutane kusan dubu daya ne suka rasa rayukansu a wannan rikici a shekaru uku da suka gabata, yayin da wasu mutanen kimanin dubu 250 suka yi gudun hijira zuwa wasu yankuna na kasar.

Mosambik Cabo Delado | Kampagne | Hilfe für den Norden (DW/D. Anacleto)
Hoto: DW

Kusan dai ana iya cewa an makara tsawon lokaci, kafin tura sojojin gwamnati zuwa yankin. Hasali ma 'yan bindiga sun fi karfin sojojin saboda rashin makamai da kayan aiki da rashin horo da kuma rashin sanin yankin sosai. A ranar Larabar da ta gabata 'yan ta'addan sun kai wa sojojin hari, inda suka hallaka wasu da dama. Dércio Alfazema masanin kimiyyar siyasa ne a Mozambik ya kuma yi tsokaci da cewa: "Wannan ya nuna 'yan ta'addar ba su takaita ayyukansu ga ta'asa ba kawai, suna kara neman wasu muhimman wurare a kasar, inda za su yi amfani da su domin kara matsa kaimi kan boyayyiyar manufarsu a kan gwamnati da babu wanda ya sani."

Dukkan kokarin gwamnati na shawo kan lamarin ya ci tura, a cewar 'yar jarida Estacio Valoli. Ta ce gwamnatin ta fara kokarin shawo kan tsaro tare da hadin gwiwa da wani kamfanin tsaro na Wagner na kasar Rasha wanda ke da alaka da fadar Kremlin, sannan kuma ta yi da wani kamfanin tsaro na Afirka ta Kudu, sai dai sai dan karen tsada ba biyan bukata. Watakila wani abu ya sauya idan Rasha ta bude sansaninta a Mozambik a cewar Valoi.

Russland Mosambik Filipe Nyusi bei Putin
Shugaba Filipe Nyusi na Mosambik da takwaransa na Rasha Vladmir PutinHoto: Reuters/Sputnik/A. Nikolsky

Rahotanni dai sun ce Rasha ta kulla dangantar soji da Mozambik da kuma wasu kasashe biyar na Afirka ciki har da batun kafa sansanin sojoji, batun da a yanzu ake ta cece-kuce a kansa a Mozambik din. Ko da yake tushen rikicin na cikin gida ne, 'yan jihadin na Mozambik suna da kawance da wasu kungiyoyi na ketare musamman ma a kasar Tanzaniya, inda gwamnatin Mozambik ta yi amannar cewa a can ne yawancin mayakan suke samun horo. A ranar 13 ga watan Nuwambar 2019 an kai hari a wani kauye da ke kusa da kan iyaka da Tanzaniyan, inda 'yan jihadin suka halaka mutane shida.

Ana daukar kasar Tanzaniya a matsayin inda masu fafutukar jihadin ke kara samun gindin zama. Kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na al'ummar Tanzaniya Musulmi ne, sabanin Mozambik inda yawan musulmin yake tsakanin kashi 18 zuwa 20 cikin 100. A halin da ake ciki dai gwamnatin ta Mozambik a birnin Maputo ta na kara nuna kwarin gwiwa, sannu a hankali sojoji ke karbe iko da yankunan da 'yan ta'addan suka mamaye. 'Yan ta'addan 59 aka kashe wasu da dama kuma aka yi musu kofar rago. Bugu da kari gwamnatin ta kuma nemi taimakon gamayyar kasashen duniya. Ministar harkokin wajen Mozambik Veronica Macamo ta sanar da cewa suna bukatar hana yi wa kasar kutse a kan iyakoki, inda a yanzu sojojin gwamnatin da na makwabciyarta Tanzaniya suke sa ido da kuma tabbatar da tsaro.