1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar yajin aikin Ma'aikata a Plateau

December 4, 2012

Ƙungiyar kwadagon Najeriya ta ba wa gwamnatin plateau wa'adin biyan albashin ma'aikata na wata biyar da suka gabata ko kuma, ta fuskanci yajin aikin gama gari.

https://p.dw.com/p/16vlE
Hoto: dapd

Hedkwatar ƙungiyar kwadago ta Najeriya ta baiwa gwamnan jihar Plateau Jonah Jang wa'adin zuwa karfe 12 na daren Litini ko dai ya biya ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar kuɗin su na albashin watanni biyar, ko kuma su kira yajin aiki na gama gari cikin jihar Plateau.

Shugaban ƙungiyar kwadago a jihar Plateau kenan comarade Jibrin bancir, ya yi bayani kan irin matakai da zasu ɗauka domin bin umurnin uwar ƙungiyar kwadago ta ƙasa dan gane da wannan takaddama da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa na tsakanin ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar Plateau da gwamnatin jihar, inda yace zasu rufe ɗaukaccin maikatun gwamnatin Plateau, zasu rufe Bankuna da gidajen mai da kuma wasu wuraren gudanar da harkokin gwamnatin jiha.

To gabanin wannan sanarwar ta uwar ƙungiyar kwadangon dai sai da shugabanin kwadago na Nigeriya suka yi wata ganawa ta sirri tsakanin su da gwamna Jang, to ko sun kasa cimma matsaya ne ya kai ga debarwa gwamnatin na Plateau wa'adi, komarade bancir yayi karin haske, inda yace gwamna Jang yayi kememe da bukatun shugabanin kwadagon na ganin cewar ya sauke nauyin bashin kuɗin albashin watanni biya da miaktan ke bin gwamnatin jiha.

Nigeria Lagos Benzin
Hoto: dapd

A ɓangare guda kuma gwamnatin Plateau ta bakin kwamishinan watsa labarai Yiljab Abraham, ta tsaya ne kan dokar ƙasa data ce duk maa'ikatan da suka shiga yajjin aiki ba zasu sami albashin su ba na tsawon lokacin da suke cikin yajin, inda tuni ma wasu rahotanni na cewar gwamnatin zata kori ma'aikatan da suka ki komawa bakin aiki, to amma kwamishinan watsa labaran ya ce ba gaskiya bane suna bukata ne kawai su cike guraben maikata tare da ƙwararrun mallaman makarantu, to amma na tambayi komishinan me yasa sai yanzu ake neman daukan sabbin maikatan? Kwamishinan yace tun hasali gwamnati na da kudirin ɗiban sabbin ma'aikata a yankunan jihar.

Wasu maikatan ƙananan hukumomi dana zanta dasu sun bayyanar min hali da suke ciki sanadin yajjin aikin, inda suka ce wahala ta ishe su, rayuwa ta zame musu cikin ƙunci, kuma babu wata hanya ta samun sauki.

Yanzu dai jama'a sun zuba ido ne suga ko wata kila za'a shawo kan wannan matsala kafin wa'adin na kungiyar kwadgo, domin kuwa sakamakon lamarin, talaka ne za'a bari cikin halin haula'i.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa

Edita : Zainab Mohammed Abubakar