Barazanar yaɗuwar cututtuka a Nepal | Labarai | DW | 30.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar yaɗuwar cututtuka a Nepal

Yanayin da ake cikinsa na gawarwarkin mutanen da ke zube barjat a kan tituna na iya janyo ɓarkewar annoba.

Jama'ar da suka tsira da rayukansu a girgiza ƙasar da ta auku a Nepal waɗanda ke yashe a waje cikin ruwa da iska.Na cikin fargaba jin tsoron yaɗuwar cututtuka kamar Kwalara da sauransu.

Ƙwararru sun yi gargaɗi cewar a irin yanayin da ake cikinsa,jama'a na iya kamuwa da cututtuka ta hanyar shan ruwan da ba shi da tsabta.Wanda kuma ka iya zama irin halin da Haiti ta samu kanta a ciki a sheraru 2010 bayan girgiza ƙasar da aka yi a can.