1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton 'yancin yin addini a duniya

Strack Christoph ZMA/LMJ
October 29, 2020

'Yancin walwalar mabiya addinai marasa rinjaye tsakanin al'umma na ci gaba da fuskantar barazana a fadin duniya, a cewar wani rahoto game da walwalar mabiya addinai.

https://p.dw.com/p/3kc7t
Koptische Christen in Ägypten
'Yancin yin addni na fuskantar barazana a duniyaHoto: picture-alliance/Arved Gintenreiter

Dangane da wannan matsalar ne dai ake kara jaddada muhimmancin tattaunawa a maimakon tursasawa. Rahoton na nuni da cewar mabiyar addinai na cigaba da fuskantar ukuba a ya yin da suke tafiyar da harkokinsu na bauta. Inda bayyana addinin krista a matsayin wadda wannan matsala tafi shafa, duk da cewar wannan matsala ce da ta shafi mabiya addinan da suka kasance daidaiku a tsakanin wadanda suka fi rinjaye. 

A cewar kwamisshinan harkokin addinai na Jamus Markus Grübel hakan bai dace ba: "Sama da kashi 80 daga cikin 100 na al'ummar duniya, kan yi ikirarin addini. Kowane dan Adam yana da 'yancin yin addini. Sai dai a kan takaitawa mutane wannan 'yanci da ke dasa ayar tambaya. Uku daga cikin hudu na mutane na zama ne a kasashen da ake taikaita musu 'yancin yin addininsu. Yin shgulgulan addini na nufin fuskantar hukunci, nuna musu wariya da azabtarwa. Kuma matsalar ta kara muni a shekarun baya-bayan nan".

Deutschland Bericht zur weltweiter Religionsfreiheit
Kwamisshinan harkokin addinai na Jamus Marrkus GrübelHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture-alliance

Grübel ya yi misali da mawuyacin hali da 'yan Musulmin Uyghur a Chaina ke ciki da kuma 'yan Rohingya na kasar Myanmar. Kazalika da bacin ran da ya mamaye shafukan sada zumunta na zamani da zanga-zanga a titunan Pakistan, bayan hukuncin da aka yanke wa wani dan Asiya kuma Krista da ya yi kalaman batanci ga fiyayyen hallitu tsira da aminci su kara tabbata a gareshi. Mutumin da daga bisani ya samu nasarar barin kasar.

Kwamishinan addinin kazalika ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda lamura ke gudanana tsakanin masu addinai marasa rinjaye a kasashe kamar Iran da Najeriya. Ludwig Schick Archbishop na Banberg, shi ne shugaban majalisar limaman darikar Katolika a Jamus: "Hakan na nufin wajibi ne mu mike tsaye wajen kare 'yancin walwalar addini. Saboda akwai koma baya sosai na 'yancin yin addini, batun da ke barazana ga zaman lafiyar duniya baki daya. Idan muna muradin zaman lafiya, wajibi ne a bayar da walwalar addini. Idan muna muradin kyakkyawar makoma, wajibi ne mu tabbatar da adalci da zaman lafiya a tsakanin al'umma".
Sai dai kuma an samu sauyi sosai a wasu kasashe a shekarun baya-bayan nan a cewar kwamishinan harkokin addinai na Jamus Gübel. Bayan juyin mulki a shekara ta 2019 a Sudan, an soke hukuncin kisa kana ana bukukuwan Kirsimeti tare da gayyatar Yahudawa da su je kasar walau domin zama ko kuma ziyara. Kazalika ya yabawa rawar da kafar yada labaran DW ke takawa wajen wayer da kan jama'a dangane da rungumar kalaman zaman lafiya tare da kauracewa kalaman batanci. 

Berlin Moschee
Masallata a masallacin Sehitlik da ke birnin Berlin fadar gwamnatin JamusHoto: Getty Images/S. Gallup

Karo na biyu kenan tun bayan shekara ta 2016, gwamnatin Tarayyar Jamus ke gabatar da rahoto dangane da 'yancin walwalar addinai a duniya. Rahoton mai shafukan 200, na zuwa ne a daidai lokacin da batun 'yancin walwalar addini ke fuskantar kalubale a kasar Faransa, tun bayan kisan wani malamain makaranta da wani matashi ya aikata.