Barazanar kungiyar IS a kasar Libiya | Labarai | DW | 02.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar kungiyar IS a kasar Libiya

A yayin da ake kokarin kafa gwamnatin hadin kan 'yan kasa a Libiya, kungiyar IS reshen Libiya na kasancewa barazana ganin yadda take kaiwa ga arzikin man fetir.

Masu ikirarin jihadin na IS a Libiya dai da ke rike da birnin Syrte, na amfani ne da yanayin da kasar ke fuskanta na rashin tsayayyar gwamnati inda sau tari suka kai hare-hare ga ma'aikatun man kasar. Da yake magana kan wannan batu na kasar Libiya, sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da ke halartar wani zaman taro a birnin Roma na kasar Italiya, ya ce a daidai lokacin da ake daf da samun gwamnatin hadin kan 'yan kasa, bai kyautu ba a ce 'yan jihadin kasar ta Libiya sun kai ga samun biliyoyin dalar Amirka daga man da suke sata ba.