Barazanar kiwon lafiya a Yamen | Labarai | DW | 31.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar kiwon lafiya a Yamen

Asibitin birnin Sana'a da ake jinyar daruruwan kananan yara da mata masu juna biyu na fuskantar matsaloli na rashin magunguna dama man fetir.

Kungiyar agaji ta Save the Children ce ta sanar da halin da gidan asibitin ya ke ciki a wannan Litanin. Mataimakin daraktan gidan asibitin din AL-Sabeen ya ce matsalar ta yi kamari fiye da yanda ba a zato. Kuma Kungiyar ta Save the Children ta ja hankalin duniya na cewa matsawar wannan gidan asibiti ya dakatar da aiki, to kuwa mata da yara kanana da dama za su mutu musamman ganin irin yanda ake ci gaba da yaki a kasar.

Kawancan kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta a cikin yakin kasar ta Yemen ne dai, ya saka takunkumin hana amfanin da gabar ruwan kasar ta Yemen wanda hakan ya haddasa matsalar karancin abinci da magunguna dama man fetir a wannan kasa.