Barazanar kisan gilla ga mata a duniya | Labarai | DW | 08.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar kisan gilla ga mata a duniya

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da shan miyagun kwayoyi da aikata manyan laifuka ya fitar, ya ce mata na fuskantar kisa a duniya.

Symbolbild Gewalt gegen Frauen (picture alliance/dpa)

Cin zarafin mata na yawaita a Afirka da Asiya

Wannan dai na kunshe ne cikin wani rahoto da ofishin ya fitar, inda ya nunar da cewa kimanin mata dubu 50 ne mazajensu ko kuma iyalansu suka hallaka a shekara ta 2017 kawai. Rahoton ya ce kimanin mata dubu 87 ke fuskantar barazanar kisa a duniya baki daya, inda ya ce mafi yawan barazanar da ma kisan sun fi a kasashen Asiya da Afirka. Mafi kasari dai mazajen ko kuma tsofaffin mazaje kan yi kisan da suka jima suna shirya yinsa ba wai bisa hadari ba. Majalisar Dinkin Duniyar ta nunar da cewa mafi akasari kisan na afkuwa ne sakamakaon kishi, wanda kuma tun daga shekara ta 2012 abin ke karuwa.