Barazanar Karzai a kan shirin tsaro | Labarai | DW | 24.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar Karzai a kan shirin tsaro

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya ce bai zai sanya hannu kan wata yarjejeniya game da wani sabon shiri na tsaro tsakaninsa da Amirka ba.

Mr. Karzai ya bayyana hakan ne a jawabinsa na rufe taron kwanaki hudu da ya yi 'yan majalisar tuntuba ta Loya Jirga wadda ta kunshi shugabannin addinai da na kabilu da kuma 'yan siyasar kasar su kimanin dubu biyu da 500. Shugaban na Afghanistan ya ce ba za'a sanya hannu a kan yarjejeniyar ba har sai bayan zaben shugaban kasar da za'a yi cikin watan Afirilun badi inda ya kara da in ba bu zaman lafiya a kasar ba amfanin amincewa da ita, don kuwa in yai hakan to shakka babu zai haifar da matsala ga Afghanistan.

Gabannin kammala taron dai shugaban majalisar ta Loya Jirga Sibghatullah Mojeddedi ya shidawa Karzai cewar muddin bai sanya hannu kan yajejeniya ba to 'yan majalisar za su yi fushi wannan mataki. Wannan yarjeejniya ta tanadi ba wa Amirka damar ci-gaba da jibge sojojinta a Afghanistan bayam dakarun NATO sun fice daga kasar a shekara ta 2014.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe