1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar hare-haren ta'addanci a Turai

March 13, 2013

Kasashen Turai sun shiga cikin barazanar hare-haren 'yan ta'adda sakamakon yaki da 'yan tarzoma da suka kaddamar a Mali.

https://p.dw.com/p/17wtt
epa03607252 French military patrol the damaged market area of downtown Gao, Mali, 02 March 2013. Chadian president Idriss Deby confirmed 01 March 2013 that a top Al-Qaeda commander, Abou Zeid, was killed in combat as French and Chadian forces continue to battle hardline Islamists in Mali's mountainous north. EPA/TANYA BINDRA
Hoto: Reuters

A wani rahoton da shugaban kwamitin yaƙi da ta'addanci na ƙungiyar Tarrayar Turai Giles de Kerchove ya gabatar da shi a makon jiya a gaban ministiocin harkokin cikin gida na ƙungiyar Tarrayar Turai , ya yi gargadin cewar sakamakon yaƙi da ƙasashen ƙungiyar suka shiga a Mali, kasashen na fuskanta barazana ta ayyukan ta'addanci daga masu ayyukan tayar da tarzoma.

A cikin rahoton wanda Gile Kerchove shugaban hukumar dake yaƙi da ta'addanci ya gabatar ya tabbatar da cewar 'yan kasashen na nahiyar turai dake yin tafiye-tafiye a cikin kasashen Afirka dama wadanda ke zaune a Turan na fuskantar babbar barazana sannan kuma akwai yiwuwar samin hare-hare na masu kai farmaki na kunar bakin wake idan har ba a tashi tsaye ba.

Ko da shike masu kishin addinin na hurta kallamun cewa manufofin da suke da shi, shine na shinfiɗa tsarin shari'a addinin musulumci, amma masu yin nazari akan al'amura da ma gwamnatin Mali na cewar dalilan yin aware sun ta'alaka ne da neman arziki da fataucin miyagun kwayoyi da makamai cikin ƙungurimin daji dake a yanki arewaci na kasar.

A convoy of Malian troops makes a stop to test some of their weapons near Hambori, northern Mali, on the road to Gao, Monday Feb. 4, 2013. French troops launched airstrikes on Islamic militant training camps and arms depots around Kidal and Tessalit in Mali's far north, defense officials said Sunday, as the first supply convoy of food, fuel and parts to eastern Mali headed across the country. (AP Photo/Jerome Delay)
Hoto: picture-alliance/AP

Misali mafi karara da ake baiyanawa akan wannan lamari na tawayen Mali da ake dangatawa da masu fataucin miyagun kwayoyin shine cewar a shekaru biyun da suka wuce, wani jirgi dauke da miyagun kwayoyi ya sauka a garin Gao ,kana wani dan lokaci kalilan wannan jirgi ya bace a cikin Hamada a yanki arewacin Mali tsakanin Kidal da Gao kafin daga bisani a taras da tarkacen jirgen a ƙone cikin Hamada.

kuma a yau gundumawar da kasashen turan ke bayarwa a Mali, domin yaƙar yan ta'adda na zama wata barazana da masu kishin addinin ke ganin ta katse hanyoyinsu ne ,na samar da kudaden shiga wanda kuma suke ganin wannan wata hujja ce ta kai hare-hare na ta'adanci akan 'yan kasashen Turai domin yin ramuwar gaya. Kobias Koep wani masanin ne akan sha'anin kimiyar siyasa na Kungiyar Tarrayar Turai, yace barazana fa akwai ta ,kuma ba mu san ba ta inda zata fito , amma da yake 'yan ta'addar na Mali na da alaƙa da kungiyar , ba wai tilas ba ne mu ce hari zai zo daga alqaida ba, ko su, abinda ya fi zama mafi wajibi shine na yin kokowar riga kafi akan abkuwar duk wata barazana, ya ce yanzu kuma bayan Afganistan, Mali ta zama wani sansanin 'yan ta'adda.

Wani abin daka iya zama hadari ga nahiyar ta Turai shine cewar yawancin wasu daga cikin wadanda ake tunani za su iya kai harin, magoya bayan kungiyar 'yan Mali suna dauke da takardun zama 'yan kasa na Mali da na wasu kasashen Turai, abinda ka iya ba su damar shiga cikin kasashen a lokacin da suka ga dama idan dai har ba a tantance su ba kamar yadda rahoton ya nuna ,wannan kuma wani babban fargaba ne a cewar wata 'yar majalisar dokokin ta Kungiyar Tarayyar Turai Franziska Brantner:

Fighters from Islamist group Ansar Dine stand guard as they prepare to hand over a Swiss female hostage for transport by helicopter to neighboring Burkina Faso, at a designated rendezvous point in the desert outside Timbuktu, Mali Tuesday, April 24, 2012. Two main groups now appear to be competing to govern northern Mali: Ansar Dine, which wants to see Sharia law brought to Mali, and separatist rebels who already have declared an independent state. (Foto:AP/dapd)
Hoto: dapd

Ta ce matsalar shine cewar kamar yadda mista Gile ne, shugaban hukumar yaki da ta'addanci ya baiyana cewar yanzu Mali ta zama sansanin, 'yan ta'ada ta ce to amma yaya za a iya a ganosu .Tun da kun ce yawancinsu suna dauke da paseport biyu na Turai da na Mali, ta ce Mali za ta kasance garesu wajan fakewa amma kuma idan suka tashi kai hare haren za su iya shiga jiragen sama su je idan suke so a turai inda ba tantance su ba.

A yanzu za a iya cewar abu biyu ne Kungiyar Tarayyar Turai ta ke yin fafutuka a kansa, na farko tabbatar da dorewa tattalin arzikin Mali ta hanyar agajin da suke bata, sannan na biyu suka kai ga cimma samar da shirin tattaunawa na 'yan siyasa da dukkannin sauran 'yan kasar domin su kai ga saka hannu akan sansani 'yan ta'adar dake bowe a yankin arewacin Mali a cikin Hamada.

Mawallafi: Abdurahaman Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal