Barazanar cutar Zika a kasar Brazil | Labarai | DW | 28.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar cutar Zika a kasar Brazil

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce janye wasannin Olympic daga birnin Rio de Janeiro ko kaisu wani wurin na daban ba zai hana yaduwar cutar ta Zika ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta yi watsi da kiran da wasu kwararru a fannin kiwon lafiya suka yi na ta janye gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ake wa lakabi da Olympics a Turancin Ingilishi, daga birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil sakamakon da barazanar cutar Zika. WHO ta bayyana wannan matsayar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce janye gasar wasannin daga birnin na Rio ko kuma canza wurin wasannin ba zai hana yaduwar cutar ta Zika ba. Masana kiwon lafiya kimanin 150 ne dai suka yi kira ga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta janyegasar wasanin guje-guje da tsalle-tsallen daga birnin Rio de Janeiro saboda cutar Zika da ta addabi kasar da sauran kasashen Amirka ta Kudu. Cutar Zika dai na janyo wa mata masu dauke da juna biyu da suka kamu da ita su haifi jarirai da nakasa.