Barazana ga dunkulewar Yukren a matsayin kasa daya | Siyasa | DW | 27.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Barazana ga dunkulewar Yukren a matsayin kasa daya

Fito na fiton da mayakan sa kai ke yi da sabbin mahukuntan Yukren na sanya fargabar ballewar kasar zuwa gida biyu.

A wannan Alhamis (27. 02. 14) ne dakaru - dake dauke da makamai suka karbe iko da majalisar dokokin yankin crimea na kasar Yukren, tare da daga tutar kasar rasha, lamarin da kuma ya harzuka sabbin mahukunta a birnin kiev, fadar gwamnatin kasar ta Yukren.

Ko da shike sabon shugaban Yukren Oleksander Turchinov ya bukaci mahukunta a birnin Moscow na Rasha da kar su janye mayakan ruwansu daga sansanin da ke tekun Bahr al-aswad, amma kuma matakin da sojoji dauke da makamai suka dauka na kwace iko da majalisar dokokin yankin na Crimea ya bata ran sabbin mahukuntan. Mayakan dai ba su gabatar da wata bukata ba lokacin diran mikiya akan ginin majalisar, amma alamu na nuna cewar, 'yan awaren da ke neman karkata zuwa ga Rasha ne.

Ukraine - zwischen Russland und der EU Flash-Galerie

Jirgin ruwan Rasha a tekun Bahr al-Aswad

Muradin Rasha a Yukren

Dama dai yankin na Crimea ne ke da mafi rinjayen wadanda ke magana da harshen Rasha, wanda kuma ke zama yankin da hambararren shugaban Yukren Viktor Yanukovich ke da rinjayen magoya baya, kuma Rasha ke da sansanin mayakan ruwanta, harma suka fara yin atisaye a wannan Larabar, wanda kuma Klaus Mommsen, tsohon jami'i kuma kwararre akan harkokin dakarun ruwa na ketare, kana marubuci ga mujallar Marine forum, ya ce muhimmancin da tekun ke da shi ne ya sanya Rasha kara shiga dumu dumu cikin lamarin:

Ya ce "Rasha na kara kulla damara kuma sun fitar da tankokin yaki a manyan sansanonin dakarunsu, amma wannan saboda tsaron kansu ne, ba wai wata anniyar kai farmaki ba ne. Sun ma fitar da jerin sunayen Iyalan da za su iya sake musu matsuguni - idan har akwai bukatar haka. Sun kuma fitar da manyan jiragen ruwa domin yin wannan aikin. jiragen ruwan da ke kan tekun Bahr al-aswad, na taka rawar da ba ta kasance barazana ce ba."

Sai dai sabon shugaban na Yukren Oleksander Turchinov ya ce duk wani yunkurin da Rasha za ta yi na tsallakawa da dakarunta fiye da iyakar tekun na Bahr al-aswad, za su dauka ne a matsayin yi wa Yukren kutse.

Tuni kuma ma'aikatar kula da harkokin wajen Yukren ta gayyaci mukaddashin jakadan Rasha a Yukren domin tattaunawa, a dai dai lokacin da fito na fito a tsakanin kasashen yammacin da kuma Rasha ke neman farfado da tunanin zamanin yakin cacar- baka.

Angela Merkel und David Cameron in London

Angela Merkel da David Cameron a London

Farfadowar yakin cacar-baka

Amirka da sauran kasashen yammaci irinsu Jamus da Birtaniya, na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu dangane da yanda lamura ke rikidewa a kasar ta Yukren, inda hatta a wani taron manema labaran da fira ministan Birtaniya, David Cameron ya yi tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke ziyara a kasarsa ma, ya jaddada cewar, tilas ne kowace kasa ta kaucewa tilastawa Yukren alkiblar da za ta dosa:

Ya ce " Idan al'ummar Yukren na kaunar kyautata huldarsu da Turai, da bunkasa cinikayya da ita, to, wannan abin maraba ne. Amma ba wai batu ne na tilastawa 'yan Yukren yin zabi tsakanin hulda da Rasha ko kuma da Turai ba."

Wannan kuwa na zuwa ne yayin da sabbin jagororin na Yukren ke kokarin karfafa ikonsu, inda kuma suka samin karfin gwiwar yin haka daga sakatare janar na kungiyar kawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen:

Ya ce " Ina yin kira ga sabbin mahukuntan Yukren da su ci gaba da kokarin kafa shirin siyasar da zai kunshi dukkan bangarori domin cimma muradun dimokradiyar al'ummar Yukren."

A wannan Jumma'ar (28. 02. 14) ce ake sa ran hambararren shugaban na Yukren Viktor Yanukovich zai gabatar da taron manema labarai.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin